Mahaifar Uwar Gidan Tambuwal Sun Roƙi Wamakko Kan Matsalar Wutar Lantarki

Mahaifar Uwar Gidan Tambuwal Sun Roƙi Wamakko Kan Matsalar Wutar Lantarki

 
 

 

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko mai wakiltar gundumar Sakkwato ta tsakiya, a majalisar dattijan Nijeriya ya yi alkawalin duba matsalar wutar lantarki a garin sanyinna ta karamar hukumar  Tambuwal, wanda yake mahaifa ce ga uwargidan gwamnan Sakkwato Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal.

 

Matsalar wutar lantarkin  ta kwashe shekaru hudu kamar yadda Mai Magana da yawun al'ummar garin, Sanyinna Alhaji  Bafashi Sanyinna ya shaidawa Sanata Wamakko.

 
 Ya ce daga Marmaro har bakin lambar Yabo an katse wayoyin wutar,  hakan ya sanya suka cire tsammanin gyaran wutar anan kusa. Duk da hakan suna kira tare da mika kokon baran su ga Maigirma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da ya duba musu wannan matsalar da zimmar shafe musu hawaye.
 
Tsohon gwamnan na Sakkwato Sanata Wamakko ya ba da tabbacin duba wannan matsalar, da ganin in da ya kamata a fito mata da zimmar shafe musu hawaye.

 
Mutanen garin sun yi farincikin samun wannan labari a lokacin da Sanata Wamakko ya tsaya a Sanyinna kan hanyar sa  ta komawa sakkwato daga wata ziyarar da ya kai Birnin Kebbi.
 
Managarciya ta samu wannan bayanin ne ga Bashar Abubakar MC, Mataimaki na Musamman ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan kafofin sadarwa na zamani.
Matsalar katsewar wutar lantarki ta Sanyinna ta dade tana damun mutanen garin musamman yanda lamurransu suka tsaya a haujin more rayuwa abin da ya kai ga chajin waya sukan tafi har Torankawa a gudunmuwar Yabo domin samun biyan bukata.
Wasu muhimman mutane sun tabbatarwa Managarciya duk wanda yakamata a yi magana da shi kan wutar sun yi amma ba asamu nasara ba.
Duk yunkurin jin ta bakin kwamishina a ma'aikatar kula da bunkansa karkara ta jiha Alhaji Suleman Usman Danmadamin Isa bai samu nasara ba.

Daga Muhammad Nasir.