Maganar Tazarar Haihuwa Mu A Sakkwato Muna Tare Da Addini-----Hajiya Mariya Tambuwal

Maganar Tazarar Haihuwa Mu A Sakkwato Muna Tare Da Addini-----Hajiya Mariya Tambuwal

Uwar gidan gwamnan Sakkwato Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta bayyana cewa su duk in da addinin musulunci yake da matsaya kan tazarar haihuwa su anan suke suna biyayya kai da fata.

Mariya Tambuwal ta bayyana hakan a wurin taron yini daya da kungiyar 'Breakhrough Action' ta gudanar a dakin taro na Dan Kani a Sakkwato a wannan Laraba, a jawabin da ta gabatar ta furta cewa irin wannan taron ta saba halartarsa domin muhimmancinsa gare ta, ta kuma hada kai da kungiyoyi suna aiki tare domin kawar da cin zarafin mata a cikin al'umma.

Mariya a tabakin wakiliyarta Fatima Khalid ta ce tana alfahari da wannan taron na hada malaman addini da sarakunan gargajiya wuri daya domin samar da mafita a kawar da cin zarafin mata.

"Maganar tazarar haihuwa mu a Sakkwato muna tare da addini, amfanin tazarar haihuwa don lafiyar uwar yara ne, akwai bukatar hada hannu don kawar da cin zarafin jinsi, a kuma kyautatawa iyaye mata don ganin na ba da tawa gudunmuwa a kawar da cin zarafin mata na kafa kungiya tawa da take aiki a cikin al'umma," a cewar Mariya Tambuwal.

 Dakta Jabir Sani Maihula ya ce mun yarda da tazarar haihuwa, ba mu yarda da kaiyade iyali ba.

Dakta ya tabo batun sosai in da ya fito da bayanin cewa tazarar haihuwa na nufin samar da tsari a tsakanin yaran da za ka haifa domin sha'anin kiyon lafiya da samar da sauki ga mahaifiyar yara a wurin reno. Kaiyade iyali kuwa saboda tsoron talauci kuskure ne addini bai aminta da hakan ba, ba in da aka ce mutum ya haifi yawan kaza ya tsaya.

Dakta Sani Maihula ya ce in da kalubalen yake a tsakanin abubuwan nan guda biyu yanda za a fahimtar da gama garin jama'a domin su malamai da sauran jagorori sun fahimta, abu ne da za a samar da tsari da za a tafi tare da kowa.

Mukhtar Gaya jami'in amincewa da aiyukka a jihar Sakkwato na 'the journey so far' ya bayyana makasudin kiran taron wanda shi ne karo na biyu, an yi na farkon a jihar Kebbi, domin malamai da sarakunan gargajiya a fadin jihar Sakkwato su hadu su tattauna kan gudunmuwar mazaje a wurin tazarar haihuwa, matsayin mata a wurin zartar da hukunci, mu'amalar ma'aurata a wurin kare cin zarafin jinsi a mahangar addini da al'ada.  

Ya ce za a tabo bayanai kan cin zarafin mata da maganar annobar cutar Korona da rawar da malamai za su taka kan tsarin iyali ta hanyar al'adu da addini don cimma wata matsaya da al'umma za su aiwatar don magance matsalar cin zarafin jinsi.