Gwamnatin Neja Za Ta Kafa Hukumar Sauraren Koken Makiyaya
Daga Awwal Umar Kontagora, Minna
Gwamnatin Neja za ta kafa hukumar sauraren koke koken makiyaya a jihar. Babban darakta mai kula da ilimin makiyaya da magance rikice rikice, Ardo Adamu Babayo ne ya bayyana hakan a taron baiwa shugabannin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders reshen jihar Neja takarda kama aiki a matsayin shugabannin kungiyar ta jiha, lokacin da yake wakiltar gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello a taron kaddamar da sabbin shugabannin asabar din makon da ya gabata a Minna.
Tunda farko da yake bayani, Ardo Babayo yace daga yanzu makiyaya sun shiga cikin kasafin kudin jihar nan kamar yadda gwamna Abubakar Sani Bello ya tabbatar mana bayan wani ziyarar da shugabannin Miyetti Allah suka kai masa, yace in fada maku al'ummar Fulani suna da hakki kamar kowace kabila a jihar nan, ba wani kasafin kudi da gwamnatin jiha za ta gabatarwa majalisa sai makiyaya sun samu anfani a cikin.
Babayo, yace maganar korafin kungiyar Vigilantee da gwamnatin jiha ta kafa, gwamnatin ta fahimci ya tsaya gefe daya, saboda haka za mu yi gyara ta yadda kowace kabila a jihar nan ba za a barta baya ba wajen bada gudunmawar tsaro, kuma ta yadda wasu ba za su samu mafaka wajen cutar da wasu ba.
Ardo Babayo, yace duba da korafe korafen makiyaya yayi yawa kuma ba su da wata kafar isar da kokensu, gwamnatin za ta kafa hukuma da za ta sanya idanu tun daga matakin mazabu, kananan hukumomi da jiha dan sauraren korafe korafen makiyaya, saboda haka da zaran shirin ya fara gwamnati za ta tabbatar da hada hannu da masu ruwa da tsaki a bangaren makiyaya dan ganin sun anfanin shirin.
Da yake tsokaci a taron, shugaban kungiyar ta qasa, Alhaji Hussaini Yusuf Bosso ( Jarman Chinbi) ya jawo hankalin makiyaya da su tabbatar sun mallaki katin zama dan kasa, da katin zabe domin suna da hakkin da ya rataya a wuyan su a matsayinsu na cikakkun yan kasa masu yanci.
Bosso, yace wajibi ne sarakunan Fulani makiyaya, shugabannin kungiyoyin makiyaya da su tashi tsaye wajen jajircewa dan samar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma, muddin babu zaman lafiya, abinci da nama zai yi karancin da zai iya gurgunta tattalin arzikin kasa.
Shugaban ya jawo hankalin manoma da su daina rufe labi, musamman gonakin da ke bakin hanya dan kaucewa yin barna daga dabbobi a lokacin kiwo, yace wuraren kiwo a dazuka an killace su, wurin da ba a killacen ba ma, ba a iya shiga saboda barayin shunu da masu garkuwa da mutane, sauran gonakin da ake lallabawa wajen ciyar da dabbobi da ke kusa da garuruwa, manoma sun cinye wajen har zuwa kan kwalta, wanda hakan ba daidai ba ne ya kamata gwamnati ta sanya doka akan hakan.
Alhaji Sama'ila Rabe, kodinetan kungiyar Miyetti Allah ta kasa, ya bayyana cewar sabon shugabancin kungiyar na jihar Neja da aka rantsar yau, an ba su rikon kwarya ganin kamun ludayin su da irin jajircewar da su kayi uwar kungiya ta kasa ta amince da tabbatar masu wannan kujerar a matsayin rantsattsun shugabannin da za su jagoranci kungiyar tsawon shekaru hudu.
Sabon shugaban da zai jagoranci kungiyar a jihar Neja, shi ne Alhaji Umar Abubakar Lapai, inda kungiyar ta kasa ta amince masa ya fara aiki nan take da sauran wadanda aka kaddamar da su a jiha.
managarciya