Gwamnatin Katsina ta haramta bin wasu hayyoyin mota, sayar da dabbobi da tsoffin babura
Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari sanya wasu dokoki da zasu fara aiki a yau Talata don ganin an magance matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar.
Geamnan ya ba da umarnin rufe titin Jibya zuwa Gurbin Baure ga dukkan direbobi, ana shawartar matafiya dasu rika bin hanyar Funtua.
Haka ma an rufe hanyar Kankara zuwa Sheme ga dukkan ababen hawa na kasuwanci, yayin da aka basu shawara da su rika bi ta hanyar Funtua, ababen hawan da bana kasuwanci ba ne kaɗai za su rika bin hanyar ( Private vehicles).
Ya kuma sanar da cewa motocin dake dauko iccen ƙonawa a cikin daji dukka an haramtama masu dauko itacen.
An kuma jinkirta Sayar da dabbobi a wadannan Kasuwannin kananan hukumomin: Jibiya, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Malunfashi, Charanchi, Mai'adua, Kafur, Faskari, Sabuwa, Baure, Dutsimma da Kaita.
An haramta jigilar dabbobi daga Katsina zuwa kowace jaha a Nageriya.
Gwamnati ba ta aminta da goyon mutum ukku akan babur da kuma daukar fiye da mutum ukku a adaidaita sahu (Keke Napep) da kasuwancin tsoffin Mashina ( Second-hand motorcycles) a kasuwar Charanchi.
Sannan an kara karfafa dokar haramta zirga zirgar ababen hawan, keke Napep da Mashina daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a cikin garin Katsina, yayin da su kuma sauran kananan hukumomin daga karfe 6 na yamma zuwa 6 safe.
An kara karfafa dokar haramta Sayar da Fetur a jericcans a gidajen mai.
Gidajen Sayar da man Fetur guda 2 ne kadai aka bawa dama dasu Sayar da man da bai wuce na naira dubu biyar ba ( #5000) ga masu tukin mota a cikin wadannan garuruwan: Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa, Dandume, Musawa, Matazu, Dutsimma, Kurfi, Danja, da Kafur.
Ma'aikatan lafiya, Jami'an tsaro da yan yan jarida kadai aka yadda su hau abubuwan hawa a cikin lokutan da aka haramta hawan a bayanin da Gwamna ya rattabawa hannu da kansa.