Mahara Sun Kashe  Mutun 12 A  Jihar Katsina

Mahara Sun Kashe  Mutun 12 A  Jihar Katsina
Gov. Masari
Mahara Sun Kashe  Mutun 12 A  Jihar Katsina
Daga Comr Nura Siniya.
Wasu 'yan bindiga ɗauke da miyagun makamai sun kai mummunan hari tare da kashe sama da mutun 12 da raunata mutane da dama a karamar hukumar Batsari a jihar katsina.
Yan bindigar sun shigo garin Batsari ne a daren jiya talata tsakanin sallar magriba da Isha'i inda suka dauki tsawon lokaci suna harbe harbe kan mai uwa da wabi ba tare da wani ya kai masu dauki ba har suka gama cin karensu ba babbaka suka tafi.
Karamar hukumar Batsari na daya daga cikin garuruwan da suke fama da hare haren yan bindiga na kashe kashe da sace sacen mutane a cikin yan kwanakin nan.
Yakamata gwamnati da jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su maida hankali tare da daukar kwararan matakai da zasu kawo karshen cin zarafin da 'yan bidiga suke yima al'umma a jihar katsina.