Magoya Bayan PDP Ne Za Su Kayar Da Tambuwal Da Kansu----Idris Gobir
Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni kuma dan takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Sabon Birni da Isa Honarabul Idris Muhammad Gobir ya bayyana cewa magoya bayan PDP ne da kansu za su kayar da gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a duk kujerar da ya nema cikin zaben 2023.
Honarabul Idris a zantawarsa da manema labarai ya ce "PDP na tare da bakincikin ukubar da Aminu Waziri ya dandana masu na cin amana da rashin taimako abin da suke ciki yau kenan, ba a taba mulki da 'yan jam'iya suka shiga kaskanci da cin mutunci da kin taimaka musu irin na mulkin Aminu Waziri, duk rashin cigaban da muke ciki na rashin kasuwanci da harkar noma.
"Za ka fahimci PDP na cikin bakinciki ne a lokacin da zabe ya zo wanda kake tunanani dan PDP ne shi zai kashe ta, ba mu 'yan APC za mu kayar da PDP ba magoya bayanta za su kayar da ita da kansu, jira ka gani," a cewar Gobir.
Ya juya kan halin da jam'iyarsu take ciki ya ce "Ba wata rigima a APC Sakkwato a hade take a karkashin jagorancin Sarkin Yamma duk wadanda ke siyasa a APC suna tare da shi, fita batun maganar Abdullahi Salame don ko dan majaisar da yake yi, ba shi yakai kansa ba, wane ne yakai kansa ba tare da darajar Sarkin Yamma ba, shi Gada da ko a mazabarsa bai da tasiri kake maganar akwai wata rigima a APC.
"In dai ba managar 'yan adawa ba wace matsala ake da ita bayan an rantsar da shugaban jam'iya, sai a koma maganar Satifiket, don ba abin fadi, Isah Sadik Achida shi ne shugaban APC a Sakkwato wanda ke ganin ba haka ba, mu ba mu cikin wannan layin.
"In ana maganar APC a Sakkwato ba a maganar PDP da ta rabu gida-gida kowa da nasa jagoranci, babu jagora mutum guda, cikin shugabanin duk wanda ya fita yana kawo mata matsala, gida uku take gidan mataimakin gwamna da Ummarun Kwabo da Gidan Aminu Waziri da magoya bayansa da Gidan tsohon gwamna Bafarawa, kowanensu ji yakai da kansa da ganin shi wata tsiya ne a PDP," a cewar Idris Gobir.
Maganar za ka yi takara haka ne? "Na cancanci na tsaya takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Sabon Birni da Isa, muna da abin da za mu fadawa mutane domin ni da ire-ire na da muka damu da halin da mutanenmu suke ciki, mu muke magana akan abubuwan da ake yi wa mutanenmu, mu ke tafiya wurinsu, ka taba ganin dan PDP ya jajantawa mutanen Sakkwato ta gabas kan halin da ake ciki, ai shugabanin PDP ne ba su son mu yi magana, mun dauki kaddarar duk wani wanda ke da hannu cikin yi mana cin mutunci da halaka mu mun sanya kafar wando guda da shi.
"Siyasar wannan lokacin kai da halinka ne za a yi, in muna cikin masu rayuwa in zabe ya zo muke da nasara da yardar Allah. Shekara takwas ba mu da wutar lantarki a Sabon Birni mi gwamnatin nan za ta gayawa mutanenmu".
managarciya