Rikicin APC a Kano: Majalisar dokoki  ta yi kira ga uwar jam'iyya da ta hukunta Doguwa

Rikicin APC a Kano: Majalisar dokoki  ta yi kira ga uwar jam'iyya da ta hukunta Doguwa

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi alla-wadai wadai da munanan dabi’un shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya, Alhassan Ado Doguwa.

A ranar Litinin ne dai Doguwa ya kai wa mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar, Murtala Garo hari, yayin wani taron jam’iyyar da ya gudana a gidan mataimakin gwamnan jihar, Nasir Gawuna.

A ranar Talatar da ta gabata, Doguwa ya kuma ci zarafin Sakataren Yada Labarai na APC na Jihar, Ahmad Aruwa, tare da yin barazanar saka kafar wando daya da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Rabiu Bichi.

Dan majalisar ya kuma kai wa wani dan jarida hari yayin da yake ganawa da manema labarai a gidansa a ranar Talata.

Sai dai ƴan majalisar, a wata sanarwa da shugaban masu rinjaye na majalisar, Labaran Madari ya fitar, ya ce abin da ya faru tsakanin Doguwa da mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Murtala Garo, ya saba wa ka’idojin jam’iyyar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga shelkwatar jam’iyyar APC na jihohi da na kasa da su dauki matakin da ya dace kan Doguwa, tare da la’akari da munanan dabi’unsa da wadanda su ka wuce gona da iri.