Rikicin Wike Da Gwamnan Rivers Ya Kara Ruruwa

Rikicin Wike Da Gwamnan Rivers Ya Kara Ruruwa
 

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, inda ya bayyana shi a matsayin butulu. 

Wike, tsohon gwamnan Rivers, ya bayyana hakan ne lokacin da ya yi hira da wasu zaɓaɓɓun ƴan jarida a ranar Juma'a kan rikicinsa da Gwamna Fubara, cewar rahoton Daily Trust.
Dangantaka tsakanin Wike da Fubara ta yi tsami ne ƙasa da watanni shida da miƙa mulki a hannun gwamnan na jihar Rivers.
Rikicin dai ya yi ƙamari ne makonnin da suka gabata inda aka ƙona zauren majalisar dokokin jihar da kuma yunƙurin tsige gwamnan.
Da yake magana kan rikicin da ya addabi jihar, Wike ya bayyana cewa baya son mutane masu butulci.  
"Bari in gaya muku, ba na son butulu, ba zan iya jurewa ba. Abin da ke faruwa a yanzu shi ne abin da Odili ya ce a cikin littafinsa: 'Ka ba wa mutum mulki da kuɗi, sannan za ka san mutumin." 
"Idan ba ka ba mutum, mulki da kuɗi ba, to ba ka san mutumin ba. Duk da haka, ban damu ba saboda ni ɗan siyasa ne. 
Na san abin da wasu jihohi ke fama da su saboda bashi, amma ku je ku duba ko na bar bashi, bayanan suna nan."