Bamu haɗa baki da wata jam'iyya ba, INEC ta maida martani ga su Atiku 

Bamu haɗa baki da wata jam'iyya ba, INEC ta maida martani ga su Atiku 

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce za ta duba "Damuwar" jam'iyyar PDP game da zaben shugaban ƙasan da aka kammala ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu. 

Festus Okoye, kwamishinan yaɗa labarai na INEC, ne ya yi wannan furucin yayin da yake jawabi ga mambobin PDP da suka fito zanga-zanga a hedkwatar hukumar da ke Abuja. 
Okoye ya ce takardar zanga-zangar da suka gabatar, zai damƙa wa shugaban INEC hannu da hannu kuma za'a duba damuwar da suka hango. 
"Na karbi takardar ƙorafin ku a madadin shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu kuma na muku alkawarin zata kai kan teburinsa," inji Okoye. 
"Idan akwai wasu ƙananan batutuwa da kuke son a ɗau mataki, zamu magance su amma ina mai kara tabbatar muku hukumar zaɓe na da kunnen sauraron koken 'yan kasa." 
"Wannan hukumar ta kowa ce kuma ta 'yan Najeriya ce, INEC ba ta kulla kawance da kowace jam'iyya ba. 
Bamu haɗa baki da kowace jam'iyya ko ɗan takara ba." "Ƙawancen da muka kulla da ɗaukacin al'umman tarayyan Najeriya ne, ina ƙara gode muku bisa yadda kuka yi zanga-zanga cikin lumana."