Tinubu ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a Zamfara da Kano

Tinubu ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a Zamfara da Kano
 

Bola Tinubu, zababben shugaban kasa, a yau Litinin ya bayyana  cewa fashi, ta’addanci da kashe-kashen rashin hankali hankali ba za su samu gurin zama a Nijeriya ba.

 
Ya bayyana ra’ayinsa ne kan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara a karshen mako da kuma garin Maigari da ke karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano.
 
Tinubu ya tuna cewa an kashe jami’in ‘yan sanda na, Sufeton ƴan sanda da ɗan bijilante a harin da ‘yan bindiga suka kai a Zamfara.
 
“A harin na Kano kuma, ‘yan bindiga sun kutsa gidan wani basarake inda suka harbe shi har lahira,” in ji zababben shugaban kasar.
 
Ya kara da cewa harin da aka kai garin Maru bayan an samu zaman lafiya a Zamfara, ya kara nuni da cewa akwai bukatar a kara kaimi domin murkushe ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda gaba daya.
 
“A matsayinmu na kasa dole ne mu hada kai domin mu fatattaki wadannan ‘yan kasuwa na mutuwa da ta’addanci gaba daya. Kashe-kashen rashin hankali da ta’asa irin wannan bai kamata su kasance a kasarmu ba,” inji shi.