Sarkin Musulmi Ya Nuna Gamsuwarsa Ga Mulkin Tambuwal

Sarkin Musulmi Ya Nuna Gamsuwarsa Ga Mulkin Tambuwal

Mai martaba Sarkin Musulmi ya bayyana yadda dangantakarsu take da gwamnatin Sakkwato karkashin Aminu Waziri Tambuwal  don samar da cigaba.
Sarkin Musulmi ya nuna gamsuwarsa a wurin taron Mauludin Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo karo na 14 wanda aka gudanar a harabar Masallacin Shehu a birnin Sakkwato.

"muna aiki da gwamna hannu da hannu, karfi da karfi don taimakawa al'umma da addinin musulinci, littafan nan da muka buga gwamnati da kanta ta ɗauki nauyin buga su.
"Muna kara godewa gwamna da kokari da  aiyukkan da ake yi, muna kira ga wakilin gwamna ya mika gaisuwa da  godiyarmu," a cewar Sa'ad Abubakar. 

Ya ce ba su ganganci sai dao suna kuskure don haka  a jawo hankalinsu in an ga in da suka yi kuskure.

"Danfodiyo shugabanci ya yi ba mulki ba muma ba mulki muke yi ba, akwai bambanci yanda muke yi da yanda wasu ke yin nasu duk abin da aka fada mun ji kuma muna daukar matakai, akwai littafan da muka samu na kakanninmu guda 313, mun buga 100 da aka fassara harshen Turanci da Hausa da aka rubuta  a cikin harshen Larabci, don a san a aiyukkan da suka yi na jagoranci sabanin abin da wasu ke fada wai sun yi aiyukkan ta'addanci," kalaman Sarkin Musulmi a karon farko da ya halarci Mauludin Shehu Ɗanfodiyo