Abin da ya sa aka samu karancin Man Fetur a Sakkwato

Abin da ya sa aka samu karancin Man Fetur a Sakkwato

 
Alamu na nuni da cewa akwai karancin man fetur a kasar Nijeriya ta dalilin manyan 'yan kasuwa sun daina dauko Man saboda  farashinsa na hauhawa a koyaushe.
Wata majiya da yi magana da jaridar daily trust a ranar jumu'a ta ce wasu gidajen man ba su sayar da  man ne domin hasashen da ake da shi Man zai kara tsada kafin a fara fitar da tataccen man daga kamfanin Dangote.
NNPC a lokacin da aka tuntube shi ya ce yana da isasshen mai a kasa.
Jihar Sakkwato fetur ya yi tsada in da wasu gidaje da aka gani suna da sauki ke sayar da man naira 940 a kowace lita, akwai gidajen da  ke sayar da man kan naira 1000 a kowace lita.
Mutanen jihar Sakkwato na shan bakar wuya kan karancin man fetur ganin yanda sufuri ya kara dagawa a tsakanin jama'a, duk wanda yake son samun man da rahusa sai ya yini a gidan Man NNPC kafin ya samu, a hakan ma samun ba ya da tabbas.