Na Biya Naira Biliyan 30 Na Bashin Da Gwamnatin Baya Ta Ciyo-----Gwamnan Bauchi
Gwamnan ya ce kashi 10 na IGR an rabawa kananan hukumomi 20 don hanzarta ci gaban zamantakewa da tattalin arziki tun daga tushe. Mista Mohammed ya ce gwamnatinsa tana sake fasalin jihar kuma "tana aiki tare da hukumomin tsaro da suka dace don kare yankunanmu daga masu laifi."
Daga: Abdul Ɗan Arewa
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce gwamnatin jihar ta biya Naira biliyan 30 daga cikin basussukan da gwamnatocin baya suka ciyo.
Duk da cewa Mista Mohammed bai bayar da cikakken bayani kan jadawalin bashin jihar ba, ya ce biyan bashin an yi shi ne kan Naira biliyan 1.2 kowane wata a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Mista Mohammed ya bayyana haka ne a yayin zaman farko na majalisar zartarwar jihar ranar Litinin a Bauchi.
Ya ce gwamnatinsa "ta na yin sama -da -fadi don biyan mafi yawan ayyukanmu."
A cewarsa, kudaden shiga na cikin gida a jihar ya karu da kashi 300 cikin dari a cikin lokacin da ake nazari.
Gwamnan ya ce kashi 10 na IGR an rabawa kananan hukumomi 20 don hanzarta ci gaban zamantakewa da tattalin arziki tun daga tushe.
Mista Mohammed ya ce gwamnatinsa tana sake fasalin jihar kuma "tana aiki tare da hukumomin tsaro da suka dace don kare yankunanmu daga masu laifi."
Ya ce gwamnatinsa ta kuma "gina titin kilomita dari don inganta ayyukan sufuri a cikin birane da al'ummomin karkara."
managarciya