Babban Taron Ƙasa: APC Ta Faɗa Sabon Rikici

Gwamnonin APC sun yanke shawarar yin zama a wannan Lahadi domin tattauna halin da jam'iyar su take ciki. Ana ganin rikicin yanda za a raba muƙaman jam'iya zai sanya a ɗaga zaɓen shugabanin da aka tsara gudanarwa a watan Disamba zuwa watan Junairu don aiwatar da taron ƙasa. Rikicin raba muƙamai a yankunan ƙasa abu ne da zai iya kawowa jam'iyar na ƙasu a tun takarar zaɓen 2023.

Babban Taron Ƙasa: APC Ta Faɗa Sabon Rikici

Babban Taron Ƙasa: APC Ta Faɗa Sabon Rikici

Alamu mai karfi ya bayyana cewa jam'iyar APC mai  mulki a Nijeriya za ta tsundumacikin sabon rikici kan maganar karba-karba ta shugabanci a lokacin da ake tunkarar zaben 2023 dake tafe.
Majiya mai tushe ta bayyana cewa yunkurin da aka yi na baiwa Kudu Maso Gabas shugabancin jam'iya ya hadu da cikas jagororin siyasa a yankin ba su aminta da hakan ba.
Gwamnonin APC sun yanke shawarar yin zama a wannan Lahadi domin tattauna halin da jam'iyar su take ciki.
Ana ganin rikicin yanda za a raba muƙaman jam'iya zai sanya a ɗaga zaɓen shugabanin da aka tsara gudanarwa a watan Disamba zuwa watan Junairu don aiwatar da taron ƙasa.
Rikicin raba muƙamai a yankunan ƙasa abu ne da zai iya kawowa jam'iyar na ƙasu a tun takarar zaɓen 2023.
Zaman taron gwamnonin zai mayar da hankali kan maganar karɓa-karɓa da kuma lokacin da jam'iyar za ta yi taron ƙasa da wasu abubuwa da suka dabaibayi jam'iyarsu.