PDP ta nemi Gwamnan Sakkwato da ya soma biyan ma'aikata sabon karin  albashi 

PDP ta nemi Gwamnan Sakkwato da ya soma biyan ma'aikata sabon karin  albashi 
Jam'iyar PDP a jihar Sakkwato ta yi kira ga gwamnatin Dakta Ahmad Aliyu da ta soma biyan ma'aikata mafi karancin albashi na 70,000 ba tare da bata wani lokaci ba.
Wannan kiran na kunshe ne a cikin jawabin da Sakataren yada labarai na PDP Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar ya ce sanya hannu ga sabon tsarin albashin da shugaban kasa Bola Tinubu ya aiwatar a watan Juli abu ne da yakamata gwamnonin jihohi su kama jiki wurin aiwatar da shi don ganin sun saukakawa ma'aikata a cikin wannan tsadar rayuwa da ake ciki.
Bayanin ya nuna damuwa kan rashin sanin dalilin da ya sa Gwamnatin Ahmad Aliyu ba ta aiwatar da sabon tsarin ba kuma take ya-madidin kula da walwalar ma'aikata.
Ya ce yakamata Gwamnatin jiha ta aiwatar da sabon tsarin ganin yadda jihohin Kebbi, Lagos, Akwa Ibom, Kwara, Adamawa, Gombe, Delta, Rivers, Enugu, Kogi, Anambra, Ebonyi, Ondo,  Abia da sauransu suka yi, wasun ma sun wuce dubu 70 kuma zai soma daga watan Oktoba.
Bayanin ya fahimci ma'aikata a jihar ta Sakkwato sun fada cikin rudu domin halin matsi da ake ciki ya tafi da karkashinsu da yawa daga cikin su ba su iya zuwa wurin aiki yadda sufuri ya yi tashin gwauron zabo.
PDP haka ma ta shawarci kungiyar kwadago a jiha da ta tashi tsaye ta kwatowa ma'aikata hakkin su a fara biyan sabon tsarin albashi a jiha.