Kotun Koli Ta Zayyano Hujjojin Da Ahmad Lawan Ne Dan Takarar APC Ba Machina Ba

Kotun Koli Ta Zayyano Hujjojin Da Ahmad Lawan Ne Dan Takarar APC Ba Machina Ba

Kotun koli ta tabbatar da Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya matsayin 'dan takarar sanata na yankin Yobe ta arewa a karkashin jam'iyyar APc a zabe mai zuwa, jaridar TheCable ta rahoto. A hukunci mafi rinjaye da aka yanke a ranar Litinin, kotun kolin ta soke hukuncin kotun daukaka kara wacce ta ayyana Bashir Machina matsayin 'dan takarar kujerar sanatan Yobe ta arewa a APC. 

A hukuncin, Mai shari'a Centus Nweze ya soki yadda Machina ya bi ya kai karar gwaban babbar kotun tarayya da ke Damaturu ba tare da shaidar baka ba wurin tabbatar da zargin damfara.
A hukunci mafi rinjaye, kotun kolin ta soke hukuncin kotun daukaka kara ta shiyyar Gome wacce ta jaddada hukuncin kotun kasa wacce tace Machina ne 'dan takarar Sanatan Yobe na Arewa a APC, Channels TV ta rahoto. 
Amma yayin rarrabe hukuncin, Masu shari'a Emmanuel Agimo da Adamu Jauro, sun ce Ahmada Lawan bai yi zaben fidda gwani da na jam'iyyar APC da aka yi ranar 28 ga watan Mayu kuma da kanshi ya janye domin yin zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka ranar 8 ga Yunin 2022.
Hukuncin maras rinjaye ya bayyana cewa, yin wani zaben fidda gwanin a ranar 9 ga Yunin 2022 wanda Lawan yayi nasara, yayi karantsaye ga sashi na 84, sakin layi na 5 na dokokin zabe saboda APC ba ta soke zaben fidda gwanin da aka yi a ranar 28 ga watan Mayu ba. 
Mai shari'a Centus Nweze da ya karanto hukuncin, yace hukuncin babbar kotun tarayya a Yobe da ta kotun daukaka karar dole ne a ajiye su gefe.