Tinubu da Bai Musluntar da Matarsa ba  Ta Yaya Zai  Musluntar da Najeriya---Kashim Shettima

Tinubu da Bai Musluntar da Matarsa ba  Ta Yaya Zai  Musluntar da Najeriya---Kashim Shettima

Zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana matsayar gwamnatinsu da za a kafa game da maida Najeriya daular Muslunci. 

Idan baku manta ba, Najeriya ta dauki dumi, musamman daga kiristoci a lokacin da Tinubu ya zabo Musulmi a matsayin abokin takara; Kashim Shettima. 
An soki Tinubu ainun, inda kiristoci suka yi ta bayyana hango karshen siyasar sabin shugaban kasar a zaben 25 ga watan Faburairu. 
Da yake magana a taron lakca kan rantsar dasu, Shettima ya ce Najeriya bata bukatar wani sabon tashin-tashina, domin akwai abubuwa da yawa da gwamnatisnu za ta saka a gaba. 
Ya fadi hakan ne a Abuja a yau Asabar 27 ga watan Mayu, inda ya bayyana kadan daga abubuwan da suka sanya a gaba. Ya kuma shaida cewa, mai gidansa Tinubu yana mutunta dukkan addinai, don haka ne ma ya auri mata Kirista, kuma fasto a cocin RCCG.