Babban Buri:Fita Ta Sha Uku

Idanuwana ya zuba min wanda hakan ya sanya ni ɗan daburce wa na yi azamar duƙar da kaina ƙasa.

Babban Buri:Fita Ta Sha Uku

 BABBAN BURI


MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.


FITOWA TA SHA UKU

 A tare mukaje dasu Ahmad domin kuwa Mama maganarsu kaɗai take yi, ban jima da komawa ba muna zaune muna fira da Mama A'isha ta fita ta wanke cup ɗin da Mama tasha tea a ciki, sai gata ta shigo da saurinta tana faɗan "Anty Khady ga Yaya Haidar nan zuwa".
Gabana ne ya yanke ya faɗi domin kuwa ko ban tambaya ba tabbas nasan wanda take nufi.

Ajiye cup ɗin ta yi a ƙasa sannan ta juya da sauri ta koma ficewa daga cikin ɗakin, mamakin irin rawar jikin da A'isha ke yi na tsaya yi a cikin zuciyata har bansan lokacin da suka shigo ba, sai dai tabbas naji yanayin nan da na jeji idan har yana da guri, can na tsinkayo muryar sa yana gaida Mama da tambayar ta ya lafiyar jikin?, amsawa take yi a kunya ce wanda ina saran rashin sabo ne da ba suyi dashi ba.

Ɗago da kaina na yi daga duƙen da yake na kai kallona kansa, sanya yake cikin shadda sky blue sai sheƙi take yi , yayinda tayi luf a fatar jikinsa idan ka ganshi kamar ka sace ka gudu iya haɗuwa ya haɗu.

Gaidashi na yi idanuwana na kansa , ba tare daya juyo gareni ba hankalinsa na can gunsu Ahmad waƴanda ke na nike dashi.

Be jima ba ya yi wa Mama sallama haɗi da ajiye mata kuɗi a saman gadon a cewarsa inji Hajiya Inna.

Yana fita na miƙe nace wa Mama ina zuwa zan tambaye shi yasu Yahanazu ne, alhalin ba hakan bane a raina inason na yi masa godiyar ɗawainiyar da ya keyi damu.

Ganin yana gaf na isa gunda ya yi parking ne kuma besan ina biyansa a baya ba ya sanya ni haɗawa da gudu na isa gurinsa dai dai bakin motarsa.
Wayar dake riƙe da hannuna ne ta suɓuce ta faɗi da sauri na duƙa na ɗauko kana na miƙe da sake gaidashi ya amsamin cikin kulawa hakan kuwa ba ƙaramin mamaki ya bani ba amman saina kauda abin a raina na ce "muna godiya da ɗaiwainiya hwa mun gode sosai Allah ya bada lada".

Idanuwana ya zuba min wanda hakan ya sanya ni ɗan daburce wa na yi azamar duƙar da kaina ƙasa.

"Ta waye?", naji ya faɗa wanda hakan ya sanya ni ɗan ɗago kaina domin ganin me yake nufi.

Wayar hannuna naga ya nuno da hannunsa wanda hakan ya sanya ni gane ita yake nufi.
Cikin ɗan salon maganar da bansan lokacin dana iya saba na ce "ta Baba ce ya aramin don koda wani abu ya taso na kirasa".

Miƙomin hannunsa ya yi alamar na basa gashi kuma ya tsare ni da idanuwana ya sanya na miƙa masa ba tare dana ce komai ba.

Be jima riƙe da ita ba ya miƙomin sannan ya ce"bani hanya na wuce ina sauri gurin aiki zanje kinzo kin tare min hanya."

Ɗan zaro idanuwa na yi sannan nace "ni kuma?".
"Eh mana ko akwai wata bayan kene?".

Ba tare dana ce dashi komai na bashi hanya sannan nace "dan Allah ka gaida Hajiya Inna, ka miƙamim godiya a gareta kamin na koma".

"Kizo ma sauke ki a can kiyi mata da kanki sannan ki dawo nan", ya faɗa yana me faɗawa cikin motar.

Juyawa na yi na nufi hanyar ɗakin da Mama take ba tare dana ce dashi komai ba cike da mamakinsa "dama ashe yana magana haka?", na faɗa a cikin raina.

Da idanuwa ya bita yana me ayyana abubuwa da dama a ransa kana ya tayar da motar ya yi gaba.

Ɗakin na tura na shiga bakina ɗauke da sallama , yayinda naga Mama tana kallona ƙasa ƙasa ni kuwa na basar na nemi guri na zauna ina kallon A'isha sannan na ce "sai yaushe zaku wuce gida ne?", ɓata fuska ta yi sannan ta ce "anan zan kwana Anty Khady ke kije gida keda su Ahmad Allah gidan ba daɗi da babu ke".

"Tabb lallai yarinya inake ina iya bacci a asibiti?, Allah ki rufawa kanki asiri kije gida kiyi baccin ki lafiyar Allah" , na faɗa ina kallonta.

Yinin ranar dai gaba ɗayanmu a asibitin muka yisa, Baba a kai akai yana kirana a waya ya tambayeni ya jikin na Mama yake?, sai bayan magrib sannan ya samu shigowa cikin asibitin baya Isha'i kuwa ya haɗa kansu A'isha suka nufi gida.

Bayan nurse ta shigo ƙarfe 9pm ta yi wa Mama alura kana ta ce "tana buƙatar hutu kamin zuwa safe suga yanayin jikin nata idan da sauƙi zasu sallame mu.

Ai kuwa bata jima ba bacci me nauyi ya ɗauke ta , aka barni ni ƙaɗai a cikin ɗakin sai gadajen dake jere a ciki.

Kwatsam ina game a domin bacci yaƙi zuwarmin sai kawai naga calling ya shigo cikin wayar gaba na ne ya faɗi ganin baƙuwar number, saida ta tsinke wani kiran ya sake shigowa sannan na samu zarafin ɗaga wayar.

Ɗan jimm na yi bayan na ɗaga kiran na kara wayar a kunnena.
"Ya jikin Mama?", lokaci ɗaya naji muryarsa ta ratsa dodon kunnena.

Saurin janye wayar na yi daga kan kunne na na ƙara duba number kana na mayar a saman kunne na.
"Baki ji ba?", naji ya sake faɗa.
Ɗan lumshe idanuwana na yi sannan na buɗe su a hankali na ce "da sauƙi sosai".

"Okey Allah ya ƙara sauƙin, kiyi bacci cikin aminci", ƙitt ya kashe wayar , ni kuwa na yi azamar duba wayar ganin lallai ya katse kiran ya sanya ni sauke ajiyar zuciya kana na ce "ikon Allah, ina ya samu number kirana?."


Na jima ina tunanin lamarin kan bacci ya samu sa'ar saceni.

*#Asuba ta gari KhadynHaidar.*

★★★★★★

Yana ajiye wayar ya furzar da iska daga cikin bakinsa kana ya ce "waime ke damuna ne a kan yarinyar nan?".

Ba tare daya samo amsar tambayar daya yiwa kansa ba ya miƙe ya fito Parlourn farko inda Hajiya Inna take zaune tana a talabijin.

Zama ya yi a gefenta haɗi da cewa "ashhh, na gaji Hajiya Inna" kallonsa ta yi sannan tace "aikin ne kayi ne?", "Kedai bari yau na aikatu".

"Ai haka kullum kake cewa alhalin ni banga me kake yi ba", ɗan murmusawa ya yi sannan ya ce "wai yo meya hana ki zuwa gurin ta hannun daman ki?", "Wannan ba matsalar ka bace ai".

"Haba Hajjaju meyayi zafi haka , afuwa ƴar tsohuwas".
Taɓe baki Hajiya Inna ta yi sannan ta ce "kai akeji".

Can ta kallesa tace "wai Shalele ya isalin auren ka da yarinyar nan Safiya ne ko sun janye ne naji zancen shuru?."

"Wallahi ni bansan me suke shiryawa a kai ba Hajjaju domin kuwa ni bashi ne a gaba na ba, anawa lissafin dai kamar yadda suka gaya min yau saura kwana goma!."

Zaro idanuwa ta yi sannan tace "goma? shine basu sanar dani ba?".

"Ni bana son ki sanya abin a ranki ki barni dasu kuma dan Allah kar wacce ki gayyato a gurin bikinnan don bana son kiji kunya a cikin mutane, Allah hukuncin dazan zartas a gunsu ba karami bane kawai ki zuba idanuwa kiyi kallo, na gaya masu ba ɗaya daga cikin ƴaƴansu da zanyi zaman aure da'ita amman sunƙi so suke su ɗaura auren ni kuwa zan basu mamaki wallah", ya faɗa yana kwantar da kansa a saman kafaɗarta.

Shafa sumar kansa ta yi sannan ta ce "ni naso ka fita batunsu kawai ka rungumi matar ka idan suka daura auren dan Allah bana son tashin hankali".

Ɗagowa ya yi da sauri sannan ya ce "mata mata hwa kika ce Hajiya Inna?, Allah ya tsareni da haɗa zuri'a dasu , wallahi da kinji yadda.....sai kuma ya yi shuru yana me cije leɓensa na ƙasa da haurun sa.....

Za mu ci gaba a gobe.... 

*ƳAR MUTAN BUBARE CE!