Abin Da Babba Ya Hango:Fita Na Uku

Kasancewar duk wanda ta samu hulɗa ta keyi dashi ya sanya ba zata kawo uban cikin nata ba, shawarar liƙawa Haruna suka yanke, lokaci ɗaya suka je masa da batun cikin.....

Abin Da Babba Ya Hango:Fita Na Uku

ABINDA BABBA YA HANGO.......!


RUBUTAWA; DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.


بسم الله الرحمن الرحيم


Fitowa ta uku.

️"Sorry abokina , kasan mata zama da su sai da haƙuri don haka ka ƙara haƙuri wata rana sai labari".

Girgiza kai kawai ya yi , kana suka ɗauko maganar shigo da kayan da za'ayi jibi.


Zaune suke a cikin wani ɗaki wanda gaba ɗaya sa kayan tarkacen tsubbu ne a ciki, sai wani sunku cecen mutum baƙiƙirin dashi sai ƙaton cikin dake maƙale da jikinsa, baya sanye da komai na dangane da sutura sai wani ƙyalle daya ɗaura a ƙugunsa, buɗan idanuwa kawai ya keyi yana faman lashe baki.

Kallonsu ya yi sannan cikin muryarsa mai firgitarwa ya ce "dole ne aikin ki ya dinga gaba yana dawowa baya, mahaifiyarsa ce tsaye a kansa bata bacci kullum itace ke faman wargaza mana aikinmu."

Cikin marai raicewar murya ta ce "yanzu ya za'ayi kenan ya shugaba?."

"Idan har kina son aikinmu ya yi kyau a kansa ba makawa sai an kawar da waccen tsohuwar, muddin tana raye ba zaki taɓa cin galaba a kan ɗanta ba."

Ɗan jimm ta yi sannan ta ce "to a kawar mana da'ita don kuwa akan na mallaki komai na Ƙasim ba abinda bazan iya aikata wa ba."

Wani ƙullin magani ya miƙo mata sannan ya ce "ki tabbatar da kin sanya mata wannan a cikin abinci, da zaran taci sa to tabbas sai dai wata ba ita ba, mutanen mu basa iya tunkarar gidan sune, dasu zamu sanya domin su kawar mana da ita cikin sauƙi, amman ko wannan me sauƙi ne kije ki jarraba ki gani."

Ƙarɓar maganin ta yi sannan ta ce "godiya nake yi shugaba."

Kallonsa Hajiya Turai ta yi sannan ta ce "ni kuwa maganin farin jinin maza da mata nake nema shugaba, wanda da zaran naga mutum na nuna ra'ayina a kansa mace ko namiji su biyoni ba gardamar komai."

"Dariya ya kwashe da ita wacce ta sanya ɗakin amsawa gaba ɗaya, ya ɗauki kusan 2minutes kana ya dakata ya kalleta ya ce "Turai Turai! ba sauƙi kika ce!."

"Gyáɗa kai ta yi alamar tabbatar masa da zancen sa kana ta ce "a taimakanin dashi ko nawa ne zan bayar."

Waƴansu ruwa ya janyo daga cikin wani kwano baƙiƙirin dashi kana ya ce "ki dinga wanke fuskarki da wannan idan zaki fita , harna tsawon kwana uku, iname gaya maki ba wanda ko wacce ta isa taja dake matuƙar kika nemi biyan buƙata."

Ƙarɓar ruwan ta yi tana zuba godiya kana suka ajiye masa maƙudan kuɗaɗe suka fito.

Tafiya mai nisa suka yi kamin su kawo gunda suka yi parking ɗin motar su.

Key ta yi wa motar suka nufi cikin gari cike da murna da tunanin samun nasara.

ASALIN LABARIN

Alƙasim Shu'aibu Idrees, shine cikakken sunan sa haifaffen garin Kano su huɗu Allah ya bawa iyayensu shine babba kuma namiji, sai ƙanwarsa mebi masa Hauwa dake aure anan Kano sai kuma Shamsiya itama ta yi aure anan Kano sai ƴan biyu wato Hassana da Hussaina dake shekarar ƙarshe a secondry school ta ƴan mata dake kano.

Mahaifinsu gwargwado yana da rufin asirin Allah, dukkanin su sunyi karatun boko dana islama dai dai gwargwado.

Kamin Allah ya ƙarɓi ransa sai da ya tabbatar ya ɗaura ɗan nasa a harkar kasuwanci dama kuma yana aiki da wani babban Company da ake ji dashi a garuruwa da dama.

ZULFA'U asalinta ƴar jihar Nijar ce suna zaune ita da iyayenta acan wani ƙauye dake cikin Nijar, buzaye ne waƴanda gaba ɗaya basu da burin komai a rayuwarsu sai na kuɗi , hakan ya sanya su turota aikatau domin tasar masu kuɗi a cikin garin Sokoto dake makwabtaka da kasar tasu.

Bayan ta shiga garin Sokoto kasan cewar ba wani wanda ta sani a haka ta yi ta yawon neman wanda zai taimaka mata.

Lokacin ne ta gamu da Hajiya Turai duk da ta girmeta amman a haka suke rayuwarsu da'ita har izuwa lokacin da zaman su ya koma Kano kasan cewar a ita Hajiya Turai macece me buɗewar ido wacce ke zaman kanta.

Lokacin da suka shiga garin Kano lokacin ne idanuwan ZULFA'U suka daɗa buɗe wa , nan aka shiga wartsake wa da mazan titi.

A wajen jajibe jajibenta ne ta samo Haruna yaron wani Alh da take hulɗa dashi ne, sau ɗaya ƙaddara ta faɗa kansa ta hanyar tarayya da'ita.

Bayan watanni ta fuskanci tana ɗauke da juna biyu sosai hankalinta dana Hajiya Turai ya tashi lokacin da sukaje asibiti aka tabbatar masu da cikin ne sai dai ya yi kwari sosai.

Kasancewar duk wanda ta samu hulɗa ta keyi dashi ya sanya ba zata kawo uban cikin nata ba, shawarar liƙawa Haruna suka yanke, lokaci ɗaya suka je masa da batun cikin.

Hankalinsa ya tashi najin wannan mummunan labarin amman daga baya sai ya fawwala wa Allah komai yasa hannu biyu ya karbi abin.

Bayan wata tara ta haifo ƴarta macce wacce ko alama bata yi kama da Haruna ba, amman kasan cewar ba asan inda za'a nufa da'ita ba ala dole aka liƙawa Haruna.

Da yake bai taɓa haihuwa ba dashi har matarsa Maryama macce mai haƙuri mai kawai ci, tasa hannu biyu ta karbi yarinyar tun tana ƙanƙanuwarta taci sunan Zainab suna ce mata Baby.

Ita ke ɗaukar dukkanin ɗawainiyarsu.

Ko nawa Haruna ya ce yana buƙata bata shayin basa.

Lokacin data fara haɗuwa da Ƙasim sosai ta ruɗe a kansa, tajewa da Hajiya Turai da zancen lokaci ɗaya suka kai sunan sa gurin boka sai gashi kuwa ya kawo kansa gurinta da sunan aure.

A lokacin kuwa an sanya ranar auren Alƙasim da ƴar wan Babansa Maimunatu amman lokaci ɗaya ya ce ba zai aureta ba shi yana da wacce yake so.

Sosai akayi daru da Alh Shu'aibu kamin ya yadda akayi auren amman da sharaɗin duk abinda ya biyo baya ba ruwansa dashi har Hajiya Umma cire hannunsu suka yi akan lamarin auren.

Da yake suna zaune a family hause ne ai kuwa nan zance ya karaɗai ko ina Ƙasim buzuwa zai aura, amman a haka iyayensa suka kulle kunnuwansu suka zuba masa idanuwa, sun sai tabbata ba zaiya gane illar abinda yake da niyar yi ba sai zuwa gaba.

A haka aka sha hidimar bikin Ƙasim da ZULFA'U ba tare da sanin nata iyayen ba, don kuwa tun bayan barowarta garin nasu har yau bata wai wayi gida ba.

Sai bayan auren ne matsaloli da yawa suka fara Kunno Kai a cikin gidan.

Bata sallah sai taga dama , bata aikin gida bata dafa abinci yaso ya ɗauko ƴar aiki amman inaáh tsananin kishi ya sanya ta hana ɗaukar mata ƴar aiki duk da tana da buƙata da'ita.

Bayan aurensu da wata biyu Allah ya yiwa Alh Shu'aibu rasuwa mutuwar data girgiza al'umma da dama kasan cewarsu mutum wanda yasan yadda yake tafiyar da rayuwarsa.

Ƙiri ƙiri ZULFA'U taƙi zuwa gidan gaisuwa a haka har aka watse kwana uku bata leƙa ba, tun bayan aurensu sau ɗaya ta taɓa zuwa gidan.
A cewar ta ƴan uwansa basa sonta don haka itama bata sonsu.

Haka ya sanya mata idanuwa ko wacce safiya muaradinta ta cancaɗa kwalliya ta fice zuwa gidan Hajiya Turai daga can su wuce wurin watsewarsu.

Hajiya Umma kuwa ganin irin matar da ɗan nata ya aura ya sanya bata zauna ba ta miƙe tsaye wajen nemawa ɗan nata tsarin Allah daga sharrin ZULFA'U. A haka kuma tana yi masa addu'ar Allah ya ƙarkato mata da hankalinsa wajen su, bata da burin daya wuce taga ɗanta ya auri ƴar mutunci don samun jikoki daga tsatso mai kyau, har yau tana yi masa addu'ar mallakar Maimunatu a matsayin matar aure.

Sosai take cin duniyarta da tsinke bari ki ba wanda bata yi domin ganin ta tara abin duniya, akai akai takan je gidan Haruna diba ƴar tata wacce yanzu a ƙalla tayi shekaru shida, kana daga bisani ta cika su da abin duniya ta tafiyarta.

Kiran wayarta ya yi akan yana son ya canja wa Baby makaranta da kuma son ya saya mata ƴan kayan sawa.

Wannan ne musabbabin tashin tashinar da suke yi da Ƙasim, ta buƙaci dubu ɗari yayinda shi kuwa be jima da kwashe dukkanin kuɗaɗen sa ba ya tura domin a shigo masa da atamfofin da zai dinga sayarwa.

Wannan kenan!......

Za mu ci gaba da a gobe...


ƳAR MUTAN BUBARE.