MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta 18

MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljan, Fita Ta 18

Page 18

 

Gaba ɗaya islamiyyar ta hargitse yanda malam Aminu ke ta jibgar Bilkisu tamkar ya samu wani ƙato a filin dambe suna dambacewa. Ita kuma banda kuka babu abin da take yi, ga sauran Malaman duk sun tafi ganin filin da zasu saukar qur'ani ranar asabar dan haka suka tafi da wasu yaran dan su gyara wurin a tsara yanda komi zai tafi daidai yanda ake buƙatarsa. Shema'u ce ta ruga da gudu cikin kuka ta nufi gidansu Bilkisun dan ta kira Babansu yazo kar akashe masa yarinya da duka. Suna zaune kofar gidan shida Major Nasir sunata fira Shema'u ta zo gun a sukwane tana uban haki, ta kasama furta kalma ko ɗaya sai kukan da take yi ba ƙaƙƙautawa, Babansu Bilkisun ya  dubeta a ɗan ruɗe yana duban bayanta  ko zai ga Bilkisu itama, ganin bai gantaba yasashi tambayarta "Shema'u ina kika baro ƙawar taki ne kike kuka? Da ƙyal ta samu ta ambaci sunan Bilkisun tana nuna hanyar data biyo, harta ƙule Major Nasir ashe yanda take karkarwa taƙi bayanin yadda akai. Tsawa ya daka mata cike da masifa yake maimaita mata tambayar "Ina Bilkisu? Natsuwar dole tazo mata, ta fara bayyana abin da ke faruwa, ai basu ankaraba sai hangen Major Nasir sukai yasha kwanar titi ya nufi hanyar islamiyyar.

Dukanta yake da gaske duka bana wasa ba hatta kaiga suma amma bai sararama dukanta ba, yana san daina dukan yana hango azabar datayi masa a kangon gidan da ta kaishi. Saukar duka kawai yaji wanda sai da ya tintsira ya sake tintsirawa kansa ya fashe numfashinsa ya ɗauke ya tafi doguwar suma! Gaba ɗaya ba wanda yaga zuwansa, sai ganin wuntsular Malam Aminun kawai suka gani ya baje ba numfashi, sake fisgosa yayi zai masa wata mahangurɓar duk da a sume yake Allah ya iso da Baba gun a rikice, ya riƙe hannun Major Nasir ɗin yana cewa ya ƙyalesa hakanan ba mamaki laifi tayi masa yake hukuntata. Duƙawa yayi gabanta yana kallon yanda take sauke numfashi bayan shafa mata ruwan da akai, hannunta ya riƙe yana jin ƙuna da zugi a ƙasan zuciyarsa, tabbas ba zai ragama mutumin nan ba, dole ya hukunta shi hukunci mai girma da azaba tunda ya iya yima wadda yake so irin wannan jahilin dukan, wata ƴar kyarma-kyarma ya fara jikinsa baki ɗaya na jijjiga idanuwansa sun juye zuwa na azabar ɓacin rai. Gaba ɗaya ajin anyi shiru kowa ya razana da ganin yanayin Major Nasir ɗin musamman waɗanda suka ganesa, shi kansa Baban ya tsorata da ganin yanayin Nasir ɗin ainun. Malam Aminu kuwa yayi nisa dan haka Baba yayi saurin yayyafa masa sauran ruwan da aka shafama Bilkisun, ya buɗe ido a hankali yana tunanin miya faru dashi ne haka? Yasan dai daga cikin sirrin Bilkisu daya sani akwai na inta shigo makarantar komi na daina tasiri ajikinta na sihiri to yau meke faruwa ne haka? Ganin ya farka ga alama bai ji wani jiki ba yasa Major Nasir kafta masa wani uban marin da gaba ɗaya sai da ƙarar saukarsa ya amsa ajin, jini ne yayi tsayuwa daga fuskar Malam Aminu, Babane ya girgiza Nasir cikin faɗa yake tambayarsa "Shin kashesa zakai dan ya daketa ? Shin baka da hankali idan ya samu matsala fa ? Cike da ƙunar zuciya ya sadda kai ƙasa yana kallon fuskar Bilkisun duk tayi kumburi idanunta sunyi kanana jajir dasu, miƙewa tsaye yayi ya nufi kofa ko waige baiyi hannunsa riƙe dana Bilkisu wadda dole tasa ta bishi saboda yanayin riƙon da yayi mata bana wasa bane ba. Cike da tausai Baba ya sake zubama Malam Aminu ruwa ya dawo hayyacinsa amma fuskarsa gaba ɗaya ta sauya abin tausai abin dariya, su kansu yaran ajin jikinsu yayi sanyi ainun ganin duka biyu kacal ya sauya ma Malam Aminu kamanni zuwa na ban dariya,wasu kasa daurewa sukai sai da suka dinga sunne kai suna darawa.

Baba ya taimaka masa ya fito daga cikin ajin ya tsaida adaidaita (keke napep)zuwa asibiti dan a duba jikinsa dan yasan ba zai rasa rauni cikin jikinsa ba ga yanayin yanda yake tafiya jiri na ɗibarsa, haka suka isa asibitin Malam Aminu baisan abin da yake faruwa ba, shi dai yana da tabbacin tsafin Bilkisu bai tasiri cikin makaranta to yau ya akai hakan ? Baba keta jera masa sannu akai-akai, shikam ko baki baisan buɗewa yanda yaji laɓɓan sunyi masa mugun nauyi kamar wani dutsi ga azabar zafin da hancinsa da gefen idonsa ke masa haiƙan.

Cikin lokaci aka dubashi aka bashi maganin tsamin jiki da sauran na rage zugi da shawaran yayi amfani da ruwan zafi ya gasa jikinsa, Baba ya biya kuɗin ya sake sakashi mota zuwa islamiyyar dan bai san gidansu ba.

 

 

Tunda ya ja hannunta suka fito bai zame ko ina ba sai da ya fito daga cikin makarantar ya fiddo wayarsa ya tura message ya maida, ko kallonta bai san yi, ji yake tamkar ya koma ya sake koyama banzan hankali, suna tsaye agun yaga Baba tallabe da tsinannen ya nufi asibiti dashi, basu jima da tafiya ba aka kawo masa motarsa ya sakata ciki ya shiga shima ƙaninsa Umar ya ja motar da ƙyal ya iya gaya masa asibitin da zai kaisu.

 

Su Malam Aminu na fita ajin suka saka ihun gaske, suna kwaikwayon yanda Malam Aminu yayi tsalle ya faɗo ƙasa yayi tsit tsabar azabar da yake ji, wasa-wasa suka dinga ihu suna jin daɗin lamarin wasu na tuhumar Shema'u akan me ta kira Babansu Bilkisun bayan ta kira sojan da zai maganinsa ? Ita dai ba baka yanzu tunaninta hukuncin da Malam Aminu zai mata idan yaji itace taje ta kira masa wanda yayi masa ɓarin makauniya harya fice hayyacinsa take,kuka ta fashe da shi mai karfi wanda yasa gaba ɗaya ajin suka natsu suna kallonta "Nashiga uku idan Malam Aminu yasan nice na kira akai masa wannan dukan wallahi ya zanyi da raina ni Shema'u wallahi ban iya ɗaukar dukan da yakema Bilkisu ni sam. "Haba Shema'u ubanwa zai gaya masa anyi hakan? Ai ko tambaya yayi cewa zamuyi Babanta ne yazo da wani yayi masa haka bamu san komi ba bayan hakan. Sai lokacin Shema'u ta ware harta fara dariya suka cigaba da tsokanar yanda Malam Aminu yaji hannun maza.

 

Kafin su isa har zazzafan zazzaɓi ya rufeta, banda kyarma babu abin da take jikinta sai hucin zafi yake, abin da ya sake hautsina sa kenan yace Umar yayi kwana ya koma makarantar islamiyyar, sanin halin zuciya irinna yayan nasa yasa yayi kwana ya koma hanyar islamiyyar yana addu'ar Allah yasa an kauda Malam Aminu daga makarantar, kuma yana zuwa zai gudu danma kar yace ya kaisa gidansu Malam Aminun.

 

Sanda su Baba suka koma makarantar su Malam Surajo sun dawo daga ganin filin da zasu gudanar da saukar karatun Alqur'anin suna cikin tattaunawar ne Baba ya shiga cikin masallacin da suke tattaunawar da sallamarsa yana tallafe da Malam Aminu da rigarsa duk jini ce, fuskarsa ta ida hayewa tamkar fanke, tayi wani tul da ita.

Cikin natsuwa Baba ya kora masu jawabin abin da yasani ya ƙara da cewar itama yarinyar tana asibiti tare da yayanta Nasiru .

Shiru sukayi domin gaba ɗayansu suna da labarin yanda Malam Aminu ya takurama yarinyar akullum sai ya daketa ya wahal da ita, wanda hakan tasa aka sake masa aji aka maida malam Kabiru ajin dan kawai ya fita sabgar yarinyar ashe hakan baisa ya daina ba, to ai yau gashi ya jama kansa gaban ɗalibansa an canza masa halitta a banza.

Kawai dirin motar sojoji suka ji kafin su ankara sun faɗo cikin masallacin fuska ba fara'a sunata mazurai "Waye Aminu ? Cewar wani murɗeɗen soja, tsit akai gun ba wanda ya samu ko damar haɗe miyau.

 

Cike da mazurai ya shigo cikin masallacin ko gama shigowa baiba ya kwashe soja uku da mari yana cewa "Ba danku tsaresu na turoku ba dan ku tafi da shegen canne na turoku(ya nuna Malam Aminu da yatsa)

Sai lokacin Baba ya samu ƙwarin gwiwar yin magana "Ashe Nasiru bance kai haƙuri kabar maganar nan ba ? Ko ban isa da kai bane ba ? Hannu ya dunƙule ya kaima bango naushi ya juya ya fita sojojin suka mara masa baya ya afka motarsa yajata da uban gudu yabar Umar tsaye yana Allah kiyaye hanya, dan ko da wasa baisan daman yace ya kaisu yanda yake a haukacen nan.

Suma sojojin bayan motar Major Nasir suka rufa da gudun tsiya.

 

Anan akaima Malam Aminu jaje tare da nasihar abin da yayi bai kyauta ba aka kaishi gidansu .

 

Kai tsaye asibinsu ya nufa da ita aka bata gado ya nufi gidansu Bilkisun da sauri dan ɗaukar Inna Huraira ta zauna gunta.

 

Ita kuma Huraira alokacin ta barbaje kayan maganinta da aka bata an tabbatar mata da indai tai hayaƙin awa huɗu to zata kori duk aljannun dake zaune gidan.

 

Ta fara hayaƙin kenan ya shigo gidan a hautsine yake gayamata Bilkisu ba lafiya tazo suje asibiti tai jinyarta.

 

Wani banzan kallo tabisa dashi tana jin ko Malam ne kwance asibiti bata zuwa sai ta gama maganinta balle wata Bilkisu can.

 

 

To fa koya zata kaya tsakaninsu kenan ?

Inna dai ga dokar maganinta.

Shi kuma Major Nasir ga abin da ya kawosa .

 

Ku dai biyo Haupha dan jin yanda zata kaya .

 

Kun san Allah idan banga cmmt da yayi munba zan maidasa na kuɗi sai ku riƙe cmmt naku na riƙe kuɗina .

 

 *Taku Haupha