Ba Za Ka Iya Goge Tarihin Saraki ba saƙon Ministar Buhari Ga Gwamnan Kwara

Ƙaramar Ministan Sufuri ta Nijeriya Gbemisola Rukayyat Saraki ƙan wa ga tsohon Gwamnan Kwara tsohon shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki ta caccaki gwamnan kwara mai ci Abdurazak kan rushe ginin mahaifinsu da gwamnati ta yi.

Ta rubuta a  turakarta ta Facebook ta ce "yau kuma gwamnatin Kwara bayan ta mayar da hankali ga gina Kwara amma ina ta mayar da hankali ga rushe gine-gine mahaifina da waɗanda aka sanya sunansa a kai, waton Wazirin Illorin.
"Komi yawan gine-ginen mahaifinmu da zai rushe, tarihin Baba Saraki ba zai goge ba domin yana cikin rayuwa da zukatan mutanen Kwara.
Hakan ya nuna matsala ta shiga a tsakanin jagororin jam'iyar APC a jihar ganin yanda suke bita da ƙullin juna.