Daya daga cikin 'yan majalisar tarayya daga Sokoto na cikin kwamitin gyaran dokokin zabe

Daya daga cikin 'yan majalisar tarayya daga Sokoto na cikin kwamitin gyaran dokokin zabe
Daya daga cikin 'yan majalisar tarayya daga Sokoto na cikin kwamitin gyaran dokokin zabe

lient="ca-pub-5831765525685780" data-ad-slot="1507215029" data-ad-format="auto" data-full-width-responsive="true">

 

Zauren Majalisar wakillan tarayyar Nijeriya ya aiyana sunayen kwamitin mutum bakwai da za su hadu da takwarorinsu a majalisar dattijai domin gyara da daidaita duk wasu wurare da suke da cikas a daftarin dokar zabe da za a yiwa gyaran fuska da majalisun suka amince da hakan kafin tafiya hutu.

Mambobin kwamitin sun hada da Akeem Adeyemi wanda shi ne zai jagoranci kwamitin, sai Honarabul Abdullahi Ahmad Kalambaina(APC Sokoto) da Faleke(APC Lagos) da Aisha Dukku(APC Gombe) da Blessing Onuh(APC Benue) da Nyima Idem(PDP Akwa Ibom) da Chris Azubogu(PDP Anambra).

Haduwar kwamitin da takwarorinsu za su yi aiki tukuru ne ko da majalisa za ta dawo hutunta  daftarin dokar yana jiran sanya hannun shugaban kasa ne kawai.
Ba a sanar karara wa'adin da aka baiwa kwamitin ya kmmala aikinsa ba, majalisa ta ce ta damu kwarai daftarin dokokin zabe ya zama doka domin a gudanar da zaben 2023 ba wata hatsaniya.