Ni Da Gwamna Mun Tattauna Wasu Dubaru Da Za Mu Bi Don Kawo Zaman Lafiya a Gabascin Sakkwato----Sanata Lamido

Ni Da Gwamna Mun Tattauna Wasu Dubaru Da Za Mu Bi Don Kawo Zaman Lafiya a Gabascin Sakkwato----Sanata Lamido

Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ya ziyarci Sanata Ibrahim Lamido a gidansa dake Abuja in da suka yi  ganawa ta musamman ta dogon lokaci domin tattauna abubuwan da suka shafi tsaro a yankin Gabascin Sakkwato da jiha baki daya.
Bayan kammala ziyarar Sanata Lamido ya sanar da manema labarai abin da suka fi mayarwa hankali a tattaunawarsuu da Gwamna ya ce matsalar tsaro ce domin tana damun su gaba daya.
Sanatan ya ce "ni da Gwamna mun tattauna wasu dubaru da za mu bi don kawo zaman lafiya a gabascin Sakkwato, ba wani shugaba dake son jama'arsa su cigaba da zama cikin tashin hankali da rashin tabbas musamman wanda al'umma suka zabe shi don suna kaunarsa don sun san zai tausaya musu.
"Gwamna Dakta Ahmad Aliyu ya damu kwarai ga matsalar tsaro a jiharsa irin hobbasar da yake yi na gamsu da ikon Allah cikin hadin kan jama'a nan gaba kadan matsalar tsaro za ta zama tarihi.
"Wasu bayanai dana samu a wurin gwamna na samu nutsuwa in matakan nan suka tabbata lalle Sakkwato za ta yi bankwana da matsalar tsaro, abin bukata anan dukkan wani mai kishin jiha ya ba da gudunmuwarsa a wurin samar da zaman lafiya da cigaban jiha," a cewar Lamido
Sanata ya nemi al'ummarsa dake cikin kuncin na rashin tsaro da su kara hakuri suna sane da duk halin da suke ciki da iKon Allah wannan musibar za ta wuce sanadiyar wannan fadi tashin da suke yi domin ba su zauna ba tun sanda aka rantsar da su, Kuma ba za su gajiya ba har sai nasara ta samu waton samun zaman lafiya a Sakkwato baki daya.