Majalisar Dattawa Za ta Bi Diddikin  Yadda Aka Kashe Kudin Yaki Da Cutar Korona----Sanata  Ahmad Lawan 

Majalisar Dattawa Za ta Bi Diddikin  Yadda Aka Kashe Kudin Yaki Da Cutar Korona----Sanata  Ahmad Lawan 

 

 

Daga Babangida Bisallah, Abuja

 

 

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya ce majalisar dokoki ta tarayya za ta samar da isassun kudade a kasafin kudin shekarar 2022 don yaki da cutar Korona, tare da tabbattar da cewa an kashe kudaden ta hanyar da ya kamata. 

Lawan yayi wannan jawabin ne a ranar Litinin yayin da yake bude babban taro kan cutar Korona da kwamitin shugaban kasa akan cutar ya shirya a Abuja. 

Mai baiwa shugaban majalisar dattawa sharawa akan aikin jarida Ola Awoniyi ya fitar da sanarwar ga manema labarai a Abuja, yammacin Talatar makon nan.

Takardar ta cigaba da cewar Shugaban majalisar ya gaya ma mahalarta taron cewa majalisar za ta yi duk abinda ya kamata wajen samar da dukkan abinda ya kamata a cikin kasafin kudin 2022 don cigaba da yaki da cutar. 
Ya ce, "amma fa akwai sharadi,  dole ne wadanda za'a damka ma kudaden su gabatar da bayanan kashe kudin yadda ya kamata. 

"Zan kuma bukaci kwamitocin mu da suke aiki tukuru tare da kwamitin shugaban kasa su tabbatar sun sa ido sosai kan yadda za'a kashe kudaden idan an samar da su ga ma'aikatar lafiya ta tarayya da hukumomin ta. 
Lawan ya bawa yan Najeriya tabbacin cewar "yan majalisar dokoki ta kasa da sauran shuwagabanni a kasar nan sun dauki harkar kiwon lafiyan yan Najeriya da muhimmanci, kuma zamu ci gaba da daukar aikin mu da muhimmanci don ganin an kare jama'ar mu da samar masu da damar yin allurar ragakafin cutar".