Pantami Ya Baiwa  Al'ummar  Gombe  Buhu 8,228 Na Abinci  Domin Tallafawa Mabuƙata

Pantami Ya Baiwa  Al'ummar  Gombe  Buhu 8,228 Na Abinci  Domin Tallafawa Mabuƙata

 

Daga Anas Saminu Ja'en.

 

A jiya Asabar 27 ga watan Agustan 2022 ne Ministan sadarwa da fasaha da tattalin arziƙi na Najeriya Farfesa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, Ya samawa yankin sa tallafin kayan abinci buhu dubu takwas da ɗari biyu da ashirin da takwas (8,228) daga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

 
Kazalika, Pantami ya samo waɗannan kayayyakin ne wanda ya yi bikin damƙa su tallafin a hannun Sarakunan gargajiya da manyan malamai addinai da ƙungiyoyin al'umma, Domin rabawa talakawa musamman mabuƙata da suke cikin wani hali a faɗin jihar Gombe birni da ƙauyukan ta.
 
Shin a jihohin ku akwai ministoci da masu manyan muƙamai a gwamnatin tarayya ko kuma sun samo muku irin wannan kayan domin mabuƙatan cikin ku?