Ba Wata Ƙara Gaban Kotu Dake Tsakanina Da Mainasara----Isah Sadik Achida

Ba Wata Ƙara Gaban Kotu Dake Tsakanina Da Mainasara----Isah Sadik Achida
Shugaban jam'iyar APC a Sakkwato Alhaji Isah Sadik Achida ya musanta maganar akwai wata shari'a dake gaban kotu tsakaninsa da Mainasara Sani kan waye shuaban APC na gaskiya.
Isah Achida a maganar da yake yiwa manema labarai a ofishin jam'iyar na jiha ya ce magana ce ta waɗanda suka faɗi zaɓe don su riƙe magoya bayansu.
"kotu  ta yi watsi da ƙararsu da daɗewa, 
Mainasara ya goyi bayan shugabancina da jagoran APC a jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, maganar shari'a yaudara ce ake yiwa magoya bayan PDP, " a cewar Achida.

Ya ce a sanina ni kadai ne shugaban jam'iyar APC a jihar Sakkwato, wadan da muka yi jayayya da su Salame ne da Gada kuma sun bar jam'iyya, Mainasara da kake magana ya zo a wurina ya janye karar da yake  yi ya goyi bayan tafiyarmu.