'Yan Siyasar Riga Ne Ke Neman Tasiri A Sakkwato---Sanata Wamakko

'Yan Siyasar Riga Ne Ke Neman Tasiri A Sakkwato---Sanata Wamakko

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a hirar da ya yi da gidan jaridar Daily Trust ya bayyana rigimar APC a jihar Sakkwato da masu yinta ya ce ba wata rigima a Sakkwato, rikicin kawai ana yinsa ne a Abuja. "APC ɗaya ce a jihar Sakkwato tare da shugabanci guda amma akwai wasu mutane da ke neman suna, kar ka mance akwai 'yan siyasar Abuja masu sanya riga an sansu, suna neman suna da yin tasiri a jiharsu," a cewarsa.

Sanata ya ƙalubalanci duk wanda zai zo Sakkwato ya bincika su waye APC, ba wai kana magana kan waɗanda ko rumfunansu ba su iya kawowa ba, kuma ba su da tasiri ga mutanensu, irin waɗannan ne ake kira 'yan siyasar Abuja, suna cikin matsalar ƙasar nan.

"A Sakkwato ba mu da gwamna mai ci a jam'iyarmu tau wa ke yaƙar wani dukkan 'yan majalisar da aka zaɓa a APC ɗaya ko biyu ne suka bari mutanen Abuja na amfani da su domin yin tasiri, ba ruwanmu da wannan saboda mun san ƙarya har koyaushe tana nan ƙarya ba ta sauyawa, kowa ke goyon bayanta kuwa tana nan dai ƙarya," a cewar Wamakko.

Ya ce a tun farko sun gudanar da zaɓen mazaɓu 244, suka kuma yi na kananan hukumomi 23 komi lafiya lau, kawai sai muka ji wani ya yi nasa a Abuja, haba ta yaya za ka yi zaɓe a Abuja wannan abin dariya ne.

Wamakko ya ƙara da cewar a haka mutanen nan suka tafi kotun Abuja kan abin da ya faru Sakkwato domin akwai haɗin baki da maganar.