APC Ta Kasa Ta Sanya Barista Sa’adatu Yanusa Cikin Kwamitin Shirya Babban Taron Mata Na Kasa
Barista Sa’adatu Yanusa daga Sakkwato tana cikin mambobin kwamitin walwala(welfare) na shida daga cikin kwamitoci takwas da jam’iyar ta kaddamar domin shirya taron. Wakiliyar mata a kwamitin rikon kwarya na jam’iyar APC a Kasa Honarabul Stella Okotete ce ta sanyawa takarda jerin mutanen hannu don sanar da al’umma wadan da aka daurawa alhakin gudanar da taron cikin nasara.
Shugaban Kwamitin rikon kwarya na jam’iyar APC a matakin kasa Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya aminta da nada shugabani da sakatarori da mambobi a kwamitoci Takwas domin shirya babban taron mata na APC a Nijeriya.
Babban taron mata na kasa an shirya gudanar da shi kwana biyu 16 da 17 ga Junairun 2022 a babban dakin taro na kasa dake Abuja.
Barista Sa’adatu Yanusa daga Sakkwato tana cikin mambobin kwamitin walwala(welfare) na shida daga cikin kwamitoci takwas da jam’iyar ta kaddamar domin shirya taron.
Wakiliyar mata a kwamitin rikon kwarya na jam’iyar APC a Kasa Honarabul Stella Okotete ce ta sanyawa takarda jerin mutanen hannu don sanar da al’umma wadan da aka daurawa alhakin gudanar da taron cikin nasara.
Manufar shirya taron domin mata su ne kashin bayan kowane zabe saboda kuri’arsu tafi yawa a mafiyawan zabukkan da ake gudanarwa a Nijeriya.
APC ta ga akwai bukatar shirya taron mata domin hada karfi tare da samar da wayewar kai a tsakaninsu domin kansu da kuma jam’iya gaba daya.
managarciya