Atiku, Obi, Kwankwaso, Dole Ne Su Haɗe Don Kawo Ƙarshen Tinubu a 2027 – Lukman
Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Arewa Maso Yamma, Salihu Lukman, ya roƙi manyan shugabannin siyasa su haɗa kai don kayar da APC da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Ya ambaci Atiku Abubakar, Peter Obi, Yemi Osinbajo, Rabiu Kwankwaso, da Nasir El-Rufai a matsayin manyan ‘yan siyasa da ya kamata su haɗu domin yin tafiya tare.
Lukman, a cikin wata sanarwa, ya ce ceto Najeriya yana buƙatar haɗin kai da yin maja a tsakanin shugabannin siyasa.
Ya nuna cewa dole ne shugabanni kasance marasa son kai kuma su haɗu don inganta dimokuraɗiyyar Najeriya.
Ya buƙaci Atiku Abubakar da Peter Obi su daina fifita muradinsu na zama shugaban ƙasa, face su yi aiki don samar da haɗin kai.
Lukman ya kuma roƙi wasu shugabannin APC, kamar Rotimi Amaechi, Rauf Aregbesola, Kayode Fayemi, da Ibikunle Amosun, da su mara wa wannan yunƙuri baya.
Lukman, ya yi gargaɗi cewa idan waɗannan shugabannin siyasa ba su haɗa kai ba, yana da matuƙar wuya a iya kayar da Tinubu a zaɓen 2027, kuma na Najeriya za ta iya fuskantar matsaloli fiye da waɗanda ake fuskanta a yanzu.