Dan takarar gwamnan jihar Sokoto karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ahmed Aliyu Sokoto, ya karyata batun cewa hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta gayyace shi ko ta kama shi don amsa tambayoyi.
Yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a unguwar Mabera da ke jihar a yammacin ranar Asabar, Aliyu ya karyata cewar an kama shi saboda aikin da yayi na sakataren asusun kudi na yan sanda.
Idan za ku tuna, wasu kafafen watsa labarai sun yi zargin cewa ICPC ta tsare dan takarar na APC kan badakalar naira biliyan 12 kafin a bayar da belinsa.
Rahoton ya kuma ce an sake shi ne a madadin wani jigon jam’iyyar tare da alkawarin cewa zai dawo ofishinsu don ci gaba da amsa tambayoyi a ranar Asabar, 14 ga watan Janairu.
A halin da ake ciki, dan takarar gwamnan ya bayyana wadanda ke yada jita-jitar kamun nasa a matsayin 'yan siyasa adawa, da ke tsoron shaharar da ya yi domin sun ga shi ne mai nasara.
Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP mai adawa ce ta kitsa labarin karyan don bata masa suna, rahoton The Sun.
Ahmad Aliyu ya jaddada cewar babu wani dalili da zai sa kowace hukuma ta yaki da cin hanci da rashawa ta gayyace shi ko kama shi, domin a cewarsa bai taba aikata wani aikin asshaa ba a lokacin da yake mulki wanda zai a gayyace shi
"Na yanke shawarar kin cewa komai tunda jita-jitan ya bayyana cewa an bukaci na dawo a ranar 14 ga watan Janairu ko a kama ni. "A yau 14 ga watan Janairu, ina ta kaiwa da komowa a cikin garin Sokoto tun da safiyar yau ina ta tsammanin kamun wanda bai faru ba.
"A yanzu gani a nan unguwar Mabera da yammacin nan kuma na yanke shawarar fada masu cewa jita-jitansu ya kasance ne saboda shaharar da nake kara samu a tsakanin mutanen jihar."
Sai dai kuma, Aliyu ya shawarci 'yan siyasa da su daina siyasar kiyayya da dacin zuciya sannan sun habbaka manufofinsu.
Ya ce siyasa kamar kasa haja ce sun kasa an ki saye shi yassa suke ta fitowa da kazafi ga wadan da suka samu karbuwa.