'Yan Ta'adda Sanye da Kayan Mata Sun Sace Mutane Masu Yawa a Katsina

'Yan Ta'adda Sanye da Kayan Mata Sun Sace Mutane Masu Yawa a Katsina

 
Wasu ƴan ta’adda da suka yi shigar mata sanye da hijabi sun yi garkuwa da mutane 26 a jihar Katsina. 
Ƴan ta'addan sun kai harin ne a ƙarshen mako a ƙauyen Runka cikin ƙaramar hukumar Safana inda suka yi awon gaba da mutanen galibinsu mata da ƙananan yara. 
Wani mazaunin yankin ya ce ƴan ta'addan sun mamaye ƙauyen ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare, inda suka riƙa yin harbe-harbe, cewar rahoton manema labarai.
“A gidana kaɗai sun sace mata 10 da maza biyu. Gaba ɗaya, sun sace jimillar mutane 26 "  
Wata majiya ta alaƙanta harin da munanan ayyukan masu ba ƴan ta'adda bayanai waɗanda ake haɗa baki da su wajen yin zagon ƙasa ga ƙoƙarin gwamnati na yaƙi da ƴan ta’adda. 
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin shugaban ƙaramar hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya shaida wa manema labarai cewa an yi garkuwa da mutanen yankin 22, amma wasu sun kuɓuta. 
Ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun shammace su ne bayan sun yi baɗɗa kama sanye da hijabai. 
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, sai dai bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.