Jam'iyyar APC Ta Fitar Da Jadawalin Zaben Fidda Gwanin Kananan Hukumomi A Neja

Jam'iyyar APC Ta Fitar Da Jadawalin Zaben Fidda Gwanin Kananan Hukumomi A Neja
Daga Awwal Umar Kontagora.
A daidai lokacin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta garzaya kotu dan hana gudanar da zabukan Kananan hukumomi a farkon watan Nuwambar shekarar nan da muke ciki, wanda aka fara sauraren karar farkon satin nan mai karewa.
Ita kuwa a na ta bangaren, jam'iyyar APC mai mulki a yau juma'a ta bayyana cewar za ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarkarun kujerar kansula da shugaban karamar hukuma ranar 29-30 na watan Satumbar nan da muke ciki.
A wata takardar sanarwar da ya sanyawa hannu, sakataren yada labarai na jam'iyyar APC a jihar Neja, Hon. Labaran Sarkin Kaji, ya bayyana cewar jam'iyyar za ta fara sayar da fom ga yan takarar kujerar kansula da na shugabancin karamar hukuma a gobe asabar 24 ga watan Satumbar nan, yayin da za ta tantance yan takarkarun duk a ranar 27 ga watan nan.
Takardar ta cigaba da cewar ranar 28 kuwa za ta fitar da sunayen yan takarkarun da tantance. Kakakin jam'iyyar ya cigaba da bayyana cewar ranar 29 za a gudanar da zaben fidda gwani ga yan takarar kansula, yayin da ranar 30 ga wata za a gudanar da zaben fidda gwani ga yan takarar shugabancin Kananan hukumomi.
Tunda farko dai, kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa sun bayyana cewar babu wani dalilin da zai hana gudanar da zabukan kamar yadda sabon dokar zaben kanañan hukumomi ya nuna.
Hon. Muhammad Bello Kusharki, shugaban gamayyar kungiyoyin siyasa a jihar, yace yan majalisar dokoki na jiha ne suka yi dokar baiwa shugabannin Kananan hukumomi wa'adin shekaru uku kan karagar mulki, kuma farkon watan Disamba ne wa'adin su zai kare, maganar wasu su tafi kotu dan dakatar da zaben tamkar karo da dokokin kasa ne.