Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.
Masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC sun fara gangamin goyon bayan gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a matsayin mataimakin shugaban kasa. Da yake karin haske ga manema labarai, shugaban kungiyar, Malam Abdullahi Sulaiman, ya bayyana cewar duba da cancanta, da karbuwa a wajen jama'a a siyasan ce da zai iya bada kwarin guiwar samun kuri'u a arewacin kasar nan a wajen talaka, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ne yafi dacewa a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Abubakar Sadik Bulama, yace masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC suna dubi da dan takarar da zai taimaka wajen samun saukin tallata dan takara da kuma samun saukin tafiyar da mulki idan an kai ga nasara, saboda wanda APC ke ganin zai taimaka wajen samar da kuri'u mafi rinjaye shi gwamnan Babagana Umara Zulum, kan haka muka tashi tsaye wajen wayar da kan al'ummar kasar nan. Akwai mutane da dama da suka nuna sha'awarsu ga neman mataimakin shugaban kasa, daga bangarorin kasar musamman a arewa, amma mu dai ba mu ga kowa ba face Umara Zulum.
Kungiyar ta nemi yayan APC da su tabbatar sun mallaki katin zabe, domin duk sosyyar ka ga APC ko Osiwajo Tinubu muddin ba ka da kuri'a to ka tabbatar da ba za ka yi anfani a tafiyar ba gaba daya.
Dan APC Stakeholders Forum tana jan hankali ga jama'a da yayan jam'iyyar wanda bai samu damar nallakar katin zabe ba ya gaggauta kafin hukumar zabe ta rufe. Wanda na shi ya bata ko wani abin ya faru to ya gaggauta zuwa hukumar zabe dan samun damar baiwa APC kuri'ar da zai ba ta gagarumin rinjaye a wannan zaben.
Duk wani xan APC indai mai kishi ne ya dauki wannan aikin wayar da kai na nallakar katin zaben dan ganin mun samu gagarumin rinjaye a babban zabe mai zuwa.
Kungiyar ta jawo hankalin yayan APC da su kauda kai akan masu son kawo siyasar rudani da suke kokarin anfani da banbancin addini, Nijeriya ba maganar addini ba ne muhimmi a wannan zaben shi samar da shugabanci nagari da zai iya fuskantar matsalolin kasar nan dan magance su. Kasancewar Bola Ahmed Tinubu musulmi, Babagana Umara Zulum musulmi ba zai hana kasar cigaba duba da ire-irensu marigayi Abiola da Babagana Kingbe dukkan su musulmi ne kuma sun samu karvuwa da nasara a zubukan da suka gabata.
Idan maigirma dan takarar shugaban kasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya amince da daukar Babagana Umara Zulum a matsayin mataimakinsa, to lallai za a samu ruwan kuri'u ba sai an wahala ba.