A ranar Talata, 5 ga watan Maris, Abubakar Kyari, ministan noma da samar da abinci ya bayyana hakikanin abin da ya haifar da karancin abinci da wahalhalu a Najeriya.
Kyari ya ce safarar kayan abinci da ake yi daga Najeriya zuwa kasashen makwabta shi ne ummul haba'isin duk wani halin kunci da ake ciki a kasar.
Ministan ya kuma dora alhakin shiga matsalolin kan tsarin sake fasalin Naira da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya yi.
Ministan ya kuma dora alhakin shiga matsalolin kan tsarin sake fasalin Naira da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya yi.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Kyari ya ce canza kudin ta sa manoma masu karamin karfi sun rasa kudaden yin noma a cikin shekarar 2022/2023.
Bugu da kari, Kyari ya bayyana cewa, sakamakon rashin samun kudi a hannun manoma, daminar shekarar 2023 ba ta samar da abincin da ake bukata domin ciyar da ‘yan Najeriya ba.
Ministan wanda ya bayyana hakan yayin da ya halarci taron muhawarar ma'aikatu da majalisar wakilai ta shirya, ya kuma ce ambaliyar ruwa da ta lalata filayen noma a fadin kasar ya haifar da karancin abinci.
Yayin da ya ke kokawa kan karancin abinci a kasar, ministan ya ce annobar COVID-19 ta yi tasiri wajen raguwar noma kayan abinci a fadin duniya.
Kyari ya bayyana cewa, Shugaba Bola Tinubu, ya umurci ma’aikatar da duk masu ruwa da tsaki da su yi duk mai yiwuwa don rage radadin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.