Gwamnatin Zamfara Ta Umarci Jama'a Dasu Mallaki Bindiga Domin Kariyar Kansu

Gwamnatin Zamfara Ta Umarci Jama'a Dasu Mallaki Bindiga Domin Kariyar Kansu


Daga Aminu Abdullahi Gusau.


Gwamna  Bello Muhammed Matawalle na jihar Zamfara ya umarci ‘yan jihar sa da su nemi lasisin mallakar bindiga a jihar,  yayin da  matsalar tsaro ta ta'azzara,sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da ke addabar al’ummar jihar.


Wannan matakin da gwamnatin jihar ta dauka shi ne ‘yan kasar su kare kansu daga hare-haren da ake kai wa a kai a kai da ke haddasa hasarar rayukan ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.


Wannan bayani yana kunahe a cikin wata sanarwa ta musamman a yau Lahadi mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara


Ya ce “a yanzu gwamnati ta umurci mutane da su shirya tare da samun bindigogi don kare kansu daga ‘yan bindigar, haka zalika, gwamnati ta umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya ba wa kowa lasisi. wadanda suka cancanta kuma suke son samun irin wadannan bindigogi don kare kansu. 


“Gwamnati a shirye ta ke ta saukaka wa mutane, musamman manoman mu wajen samar da muhimman makaman kare kansu.“Gwamnati ta riga ta kammala shirye-shiryen raba fom 500 ga kowace masarauta 19 da ke jihar domin masu son samun bindigogi don kare kansu.


;Dole ne mutane su mallaki lasisin mallakar bindigogi da sauran makaman da za a yi amfani da su wajen kare kansu.


.Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya an samu tabarbare tsaro a 

 yankunan Mada, Wonaka, da Ruwan Bore a karamar hukumar Gusau, da kuma masarautar Yansoto a karamar hukumar Tsafe.