Babangida Na Goyon Bayan Sabuwar Najeriya

Babangida Na Goyon Bayan Sabuwar Najeriya

Tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida ya yi alƙawarin cigaba da goyon bayan sa ga ƙungiyar Team New Nigeria, domin tabbatar da cikar burin manufofin kafa ƙungiyar. 

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne yayin da yake tarbar tawagar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Dr. Modibbo Yakubun Farakwai wanda ya ziyarce shi a gidan sa da ke garin Minna a Jihar Naija. 

A wata sanarwa da ta fito daga Babban Sakataren Watsa Labarai na Ƙungiyar na Ƙasa Dr. Shuaib Muhammad Tettes, an bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar shi ne uban ƙungiyar Team New Nigeria tun bayan da ya amince da shigar da shi ƙungiyar da aka yi cikin watan Oktoba na shekarar da ta gabata. 

Tun da farko, sai da shugaban ƙungiyar ya yabawa tsohon shugaban ƙasar bisa amincewa da ya yi ya zama Babban Uban Ƙungiyar da ake yi wa laƙabi da TTN a taƙaice. 

Ya nemi cigaba da samun haɗin kai da goyon bayan tsohon shugaban ƙasar wajen ba da shawarwarin da za su taimakawa manufofin ƙungiyar na inganta tsarin dimukraɗiyya da ayyukan bunƙasa rayuwar al'umma. 

Dr. Farakwai, ya bayyana cewa, ƙungiyar na mayar da hankali ne wajen ƙarfafa gwiwar matasa wajen samun horo kan sana'o'in dogaro da kai, da kuma ƙarfafa musu gwiwa kan riƙo da halayen ƙwarai, kyakkyawar tarbiyya da ba da gudunmawa don samun sauyi a siyasar ƙasar nan. 

Kungiyar ta je wannan ziyara ne, gidan tsohon shugaban ƙasa tare da rakiyar wasu jiha jigan ýan ƙungiyar.