An rufe layukkan sadarwa a ƙananan hukumomi 14 na jihar Sokoto
An rufe layukkan waya a ƙananan hukumomi 14 a jihar Sakkwato a wani ɓangare na shawo kan matsalar tsaron jihar.
Da yake sanar da daukar mtakin, Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwa ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, ya ce kananan hukumomin da aka katse hanyoyin sadarwarwar su ne suka fi fuskantar bazarar hare-haren ’yan bindgia.
A cewar Tambuwar, gwamnatin jihar ya cewa samu amincewar Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami kan daukar matakin, duba da nasarar da aka samu bayan katse hanyoyin sadarwa a makwabciyartsa, Jihar Zamfara.
Tambuwal ya ce, “Nasarar da sojoji suka samu a Zamfara ya sa sa ’yan bindiga tserewa suna shigowa jihar Sakkwato,” shi ya sa aka toshe layukan sadarwa a Kananan Hukumomin da suka hada da Tangaza, Tureta, Isa, Rabah, Goronyo da Dange Shuni.
Sauran su ne Tambuwal da Keɓɓe da Shagari, Illela da Gudu da Wurno da Sabon Birni da Gada.
Rufe layin sadarwa da sauran matakan da aka dauka a Jihar Zamfara, inda sojoji ke ci gaba da yi wa ‘yan bindiga luguden wuta, ya sa bata-garin kutsawa zuwa wasu sassa na Jihar Sakkwato, suna garkuwa da mutane suna kashe wasu tare da satar kayan abinci.
Rufe layukkan ya zowa Sakkwatawa da ba za ta ganin ba su yi tsammanin rufe layukkan a wannan lokaci.
managarciya