Mun Gamsu Da Wakilcin Wamakko Kan Haka Ya Cigaba A 2023---Mutanen Sakkwato 

Mun Gamsu Da Wakilcin Wamakko Kan Haka Ya Cigaba A 2023---Mutanen Sakkwato 

 

Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattijai Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya samu amincewa da goyon baya ga mutanen yakninsa na Sakkwato ta Arewa saboda gamsuwa da wakilcin da yake masu a majalisar dattijan Nijeriya.

"Mun gamsu da wakilcinka kan haka ka cigaba a 2023 domin kara samun romon dimukuradiyya kamar wasu yankunan Nijeriya da suka samu gwarzo mai kishin jama'a kamarka"

Sanata Wamakko ya samu damar zama dan takarar Sanata a jam'iyar APC da zai wakilci Sakkwato ta Arewa a karo na uku a 2023, an zabe shi ne ta hanyar tabbatarwa domin ba wani da ke jayayya da shi. 
Wakillai waton delegate daga yankin sun bayyana tabbatarwar bayan daya daga cikinsu da ya fito daga karamar hukumar Sakkwato ta kudu Babangida Dan Tsoho ya sanar da kudirin haka sai Aliyu A. Sabo daga Kware ya bayyana amincewarsu a madadin wakillai 420.
Alhaji Muhammad Bello Sifawa ne ya jagorancin kwamitin zaben ya ba da sanarwar cewa Wamakko shi kadai ne ke takara baya da abokin hamayya don haka ya yi nasarar samun tikitin takarar Sanata a APC. 
Wakilin APC Barista Turner ya ce zaben Sanata Wamakko ya nuna yana tare da mutanensa kuma suna jin dadinsa. </d iv>
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko  a kalamansa bayan ya samu nasara ya godewa wakillan da suka zabe sa 420 ya yi masu alkawalin zai kara kaimi wajen samar da romon dimukuradiyya a yankinsa. 
Ya yi kira ga magoya bayan APC su cigaba da goya mata baya a kowane bangare don samun nasara. An kammala zaben ne a gaban wakiliyar hukumar zabe ta kasa INEC Barista Hauwa'u Aliyu Kangiwa da sauran jamai'an tsaro.