Lokaci ya yi da yakamata a daina siyasar kudi da son kai----Honarabul S/Adar

Ɗan majalisar tarayyar Nijeriya mai waƙiltar ƙananan hukumomin Gada da Goronyo Honarabul Musa Sarkin Adar ya bayyana cewa kawar da siyasar kuɗi da son kai a Nijeriya haƙƙi ne da ya rataya kan duk wani mai kishin ƙasa.

Lokaci ya yi da yakamata a daina siyasar kudi da son kai----Honarabul S/Adar
Lokaci ya yi da yakamata a daina siyasar kudi da son kai----Honarabul S/Adar
Daga Muhammad Nasir
Ɗan majalisar tarayyar Nijeriya mai waƙiltar ƙananan hukumomin Gada da Goronyo Honarabul Musa Sarkin Adar ya bayyana cewa kawar da siyasar kuɗi da son kai a Nijeriya haƙƙi ne da ya rataya kan duk wani mai kishin ƙasa.
Sarkin Adar a hirarsa da gidan TV na ARISE ya ce lokaci ya yi da yakamata a kawar da siyasar kuɗi da son kai "Nijeriya kusan siyasar aƙida ta wuce dukan jam'iyyunmu na ƙasa ba su da wani bambanci a tsari da gudanarwa, jam'iyun son kai na 'yan takara ya mamaye su kowa dai ya ci zaɓe ba ruwansa da cigaban dimukuraɗiyya a ƙasa, shi dai gudunmuwarsa ya ci zaɓe ya samu kujera ya haye ita ce kawai aƙidar."a cewarsa. 
Haka kuma ya ci gaba da cewa mafiyawan 'yan siyasa a ƙasar nan ba su da wata ƙwarewa a fannin kawai dai sun tsinci kansu ne a siyasar don haka aka cefanar da tsarin siyasar ta koma jari hujja.
"Manema labarai yakamata su faɗakar da mutane su daina karɓar kuɗi don su yi zaɓe, ko mu 'yan siyasa mun gaji da wannan tafiyar, ba ka iya tsayawa takara ka ci zaɓe ba tare da ka kashe maƙudan kuɗi ba, muna fatar a kawar da wannan lamari a nan gaba cikin siyasar Nijeriya." in ji Honarabul S/Adar.
Da ya juya kan maganar takarar shugaban ƙasa a APC ya ce har yanzu jagoran jam'iya a ƙasa Bola Tinumbu ne kan gaba a duk masu son yin takarar amma idan Jonathan ya shigo jam'iyar za su fafata ne don neman tikitin takarar domin tsarin mulki ya ba su damar duk wanda yake son ya tsaya takara zai iya yi.