Kakale Shuni ya roki NCC su rufe layukkan waya a kananan hukumomi 3 na Sokoto

Dan majalisar wakillan Nijeriya ya yi kira ga hukumar sadarwa ta kasa NCC da ta rufe layukkan sadarwa a kananan hukumomi uku dake jihar Sokoto.

Kananan hukumomin su ne Bodinga da Dange Shuni da Tureta dake kan iyaka da jihar Zamfara. 
 
Kiran ya zo ne a lokacin da dan majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Bodinga da Dange Shuni da Tureta Honarabul Balarabe Shehu Kakale a zaman majalisa na Laraba  ya bayyana kudirin goyon baya kan muhimmancin da ke akwai na darajjanta mutane.
Ya ce akwai bukatar yankewar a kananan hukumomin duba da yanda matsalar tsaro ke ta'azara a sati nan da suka gabata.
A cewarsa lamarin ya kazanta a garuruwan Galma da Dutse da Buleri a gundumar Wababe a tsakanin 1 ga Satumba zuwa 3.
Ya cigaba da cewa an sake kai wani harin na 'yan bindiga a kauyukkan Jibuwal da Fajaldu da Waramu da Bissalam da Illelar Bissalam a gudumar Dange. An kai Tauma cikin karamar hukumar Bodinga, bayan wanda aka kai a Lambar Tureta wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 10. 
  Kakale ya fahimci kananan hukumomin uku suna da iyaka da garin Bakura da Maradun da Shinkafi a jihar Zamfara matakan da sojoji ke dauka kan 'yan bindigan ke sanya suna tsallakowa zuwa makwabtan jihar.</div
Dan majalisar ya ce kan ta'azarar aiyukkan maharan sama da magidanta  100 da mutum 500 suka bar gidajensu a Tureta da Dange Shuni suna neman taimako a jihar Sakkwato.
Majalisar tarayya ta yi kira ga hukumar tsugunar da 'yan gudun hijira ta taimakawa mutanen a wuraren da suka koma, haka ma hukumar ba da agajin gaggawa su samar da abubuwan jinkai ga mutanen.
Daga Sadiya Attahiru