PDP Ta Hango Abin da Zai Faru Idan ba Ta Karbi Mulki ba a 2027 

PDP Ta Hango Abin da Zai Faru Idan ba Ta Karbi Mulki ba a 2027 

 

Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na PDP ya fara hango nasarar da jam'iyyar za ta iya samu a zaɓen 2027. 
Kwamitin na NWC ya ba da cikakken tabbaci cewa jam'iyyar za ta ƙara yawan gwamnoninta a jihohi da kuma sake samun mulki a matakin tarayya a shekarar 2027. 
Kwamitin na NWC ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin ziyara ga gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, a gidansa na Sampou, da ke cikin ƙaramar hukumar Kolokuma/Opokuma. 
Da yake magana a madadin kwamitin NWC, ma'ajin PDP na ƙasa, Alhaji Ahmed Yayare, ya bayyana cewa saboda rashin jin daɗi da ake fuskanta a duk faɗin ƙasa, PDP za ta samar da gwamnonin jihohi masu yawa a shekarar 2027. 
"Ƙorafin yunwa da talauci ya yi yawa sosai a ƙasar. APC ba za ta iya fita yawon neman zaɓe ba domin za su sha jifa." 
"Jihohi 36 na Najeriya suna neman dawowar PDP. Babu abin da zai hana PDP ta samar da shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa a shekarar 2027."