Kwamishinan Tambuwal Mai Ci Yabar PDP Ya Koma APC

Kwamishinan Tambuwal Mai Ci Yabar PDP Ya Koma APC

 

Kasa da kwana daya da ficewar Shugaban karamar hukumar Mulkin Tangaza Hon Isah Salihu Bashar Kalanjine daga Jam'iyyar PDP  zuwa  APC,  kwamishina Mai ci a Gwamnatin Jihar Sokoto ta Aminu Waziri Tambuwal, Kanar Garba Moyi Isa ya ayyana ficewar sa daga PDP zuwa APC.

 
Kanar Garba Moyi dai ya yi  zaman kwamishina a Ma'aikatar Samar da ayukka da tsaro na Jihar sokoto ya bayyana cin Amana da rashin gaskiya da zalunci a matsayin dalilan sa na barin Jam'iyyar PDP.
 
Kanar Garba Moyi ya kara da cewa ya yanke shawarar shiga Jam'iyyar APC ne wacce ke karkashin jagorancin Maigirma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman sokoto ne saboda adalcin sa da karimcin sa.
 
Ya Kara da cewa yana sha'awar yadda Sanata Wamakko ke shugabantar Jama'a bisa adalci da rikon Amana.
 
Daga bisani kwamishinan ya bayyana ficewar sa a zaman Dan Jam'iyyar PDP kana ya ajiye kujerar sa ta kwamishinan tsaro da Samar da ayukka.
 
Da yake karbar sa a Gidan sa dake unguwar Gawon Nama Sokoto, Maigirma Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman sokoto ya bayyana samun kwamishina Moyi a Wannan tafiyar da cewa abin ci gaba ne.
 
Kana ya kara da yin Kira a gare shi da ya dukafa ga aikin ganin Nasarar Jam'iyyar APC a Gabascin sokoto da Jihar Sokoto Baki daya a zaben shekara Mai Kamawa a kasar nan 2023.
 
A lokacin ziyarar ta kwamishinan, yana tare da rakiyar Dan takarar kujerar Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto Hon. Idris Muhammad Gobir da Dan takarar Sanata a yankin Gabascin sokoto Hon. Ibrahim Lamido Isah da Dan takarar kujerar Majalisar tarayya Kananan Hukumomin Isa da Sabon Birni Hon. Abdulkadir Jelani Danbuga da kuma Shugaban Jam'iyyar APC na Yankin sabon Birni Alh. Yawale Sarkin Baki.