Limami Ya Fusata a Mimbari, Ya Soki Malaman da Suka Tallata Tikitin Muslim Muslim

Limami Ya Fusata a Mimbari, Ya Soki Malaman da Suka Tallata Tikitin Muslim Muslim

 

Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemu wanda aka fi sani da Iman Kandahar ya yi huduba da ta zagaye kusan ko ina. 

Yanzu haka ana yawo da hudubar Juma’ar da Sheikh Abubakar Umar Musa Rijiyar Lemu ya gabatar a ranar Juma’ar da ta gabata.
A Facebook Anwar Ahmad Chedi ya gutsuro bangaren hudubar inda aka ji limamin ya maida hankali a kan wasu abokan aikinsa.
Limamin masallacin na Abdullahi Ibn Abbas da ke unguwar Rijiyar Lemu ya yi Allah-wadai ne da dabi’ar wasu malaman musuluncin. 
Hudubar ta shafi halin da kasa ta ke ciki ganin yadda matasa su ka fito zanga-zangar lumanar da ta rikida ta zama tashin tashina. 
A hudubar da ya gabatar a masallacin da ke Rijiyar Lemu a Kano, ya daura kason laifi a kan malaman da suka tallata APC a 2023.
Ana zargin wasu malaman musulunci su ka fito da karfinsu wajen ganin an zabi Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben bara. Kamar yadda aka ji a bidiyo, malamin ya ce dole talakawa su san ciwon kansu, su daina yin zabe saboda sun karbi abin duniya. 
"Wanene zai kawo gudumuwa, zai kawo agaji, zai taimaka, zai kawo dauki da gyara ga al’umma? Shi ya kamata a zaba." 
"Ba kowane awon igiya ya zo shikenan ba. \
A nan su ma wasu da yawa daga cikin wadansu malamai sun zama mutanen banza da wofi." 
"Sun fito wai muslim-muslim bayan karya su ke yi, babu wani muslim-muslim, an zo an saye ku saboda abin da za ku lasa." "Saboda talaucin zuciya kun zo ku na wani muslim-muslim, shiyasa idan kun je gaban shugaban kasar, ba ya ganin kimarku saboda kun zama leburorinsu."