A Yau  Za a Ƙaddamar Da Littafin Raƙiba Da Karima A Kaduna

A Yau  Za a Ƙaddamar Da Littafin Raƙiba Da Karima A Kaduna

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

A yau Asabar ne  za'a kaddamar da tagwayen littafai guda biyu, wato Raƙiba da Karima wanda Kwararriyar ma'aikaciyar Banki nan Fatima Abba Gana ta rubuta,

Taron wanda za'a yi shi  Asabar a dakin taro na Absynia dake Hotal 17,  lamba 6 kan titin Tafawa Balewa a cikin birnin Kaduna,

Fatima Ibrahim Abba Gana dai Kwararriyar Ma'aikaciyar Banki ce inda ta yi aiki a Bank PHB daga nan ta yi aiki a bankin Keystone Bank da kuma Bankin Jaiz, yanzu haka i ta ce  MD a  kamfanin Shawullam Nigeria Limited, 

Fatima ta ce Raƙiba littafi ne na soyayya da ya ke nusantarwa akan soyayya, kuma ya da shafi 500,

Yayin da shi kuma Littafin Karima ya ke dauke da labarin matashiyar yarinya da ta kamu da son wani matashin talaka da ke maƙotaka da gidansu, kuma yana dauke da shafuka 100,

Mai sharhin littafi shi ne Farfesa Salisu Ahmad Yakasai na Jami'ar Usman Danfodiyo Sokoto,

Yayin da shugaban taro zai kasance Alhaji Mainasara Idris Sarkin Maska Hakimin Funtua, sai kuma uwar taro da  za ta zama Hajiya Hadiza Isma El-rufa'i,

Kazalika taron zai samu halartar mai masauki baki Dr. Muhammad Wakili OON, Acis,

Sannan ana sa ran halartar Gwamnoni kamar na jihar Yobe Mai Mala Buni da na Borno Farfesa Babagana Umara Zulum sai kuma na jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufa'i.