Babban Buri:Fita Ta Sha Biyu

Har lokacin Mama bata farko ba kuwa, na buɗe kular da suka shigo da'ita domin ganin abinda ke ciki.

Babban Buri:Fita Ta Sha Biyu

 BABBAN BURI

MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.

FITOWA TA SHA BIYU.


`````Ganin kamar bata numfashi ne ya sanya ni duƙewa a gurin kana na saki wani marayan kuka, ina duƙe a gurin Baba dasu Umar da A'isha suka shigo gidan ko wanensu ka kalli fuskansa zaka tabbatar a kiɗime yake.

Ɗakin suka faɗa su dukansu inajin basu ma kula dani ba a gurin.

Miƙewa nayi nima na mara masu baya, kallona Baba ya yi sannan ya ce "suma ne ta yi maza ɗauko hijabinki muje asibiti" hijabina dake yashe a ƙasa na zara nasa sannan na sawa Mama nata, zuwa lokacin Baba ya fita domin samo napep a waje.

Be jima ba ya dawo da hanzarinsa ya ɗauke ta muka biyo bayansa su Ahmad sai kuka suke yi har A'isha sai faman sharce hawaye take yi.

Kallonsu na yi nace "kuje gida ku jiramu yanzu zamu dawo kuma ku daina kuka kuyi mata addu'a", sannan na shige napep me napep yaja mu .

Kai tsaye asibiti aka wuce damu, da shigarmu a kayi hanzarin ƙarɓarta ganin yana yin da take ciki.

Gefe muka koma daga ni har Baba muna zuba idanuwana muga ta gunda ma'aikaciyar lafiya zata ɓullo domin mu tambayeta.

★★★★★★

Hankalin Hajiya Inna ya yi matuƙar tashi na rashin ganin na na fito aiki yau, wannan shine karo na farko dana yi fashin zuwa aiki tun farkon fara aikina a ƙarƙashin su.

Har gurin su Yahanazu take suka sheda mata yau basu gannin ba, iya tashin hankali ta shigesa.

Fitowa ta yi daga sashen ta nufanto baki get, a gurin da ta tsinkayo su Baban Gida direba ta nufa, tunkan ta kai gunsu suka taso su dukansu suna tambayarta lafiya kuwa da kanta.

Kallon Baban Gida ta yi ta ce "yarinyar nan ce Hadeejatu yau bata zo aiki ba abinda bata taɓa yi ba, nasan kasan gidansu ai dan Allah kaje ka dibomin lafiya kuwa?".

Nan suka fara magana a kaina kan cewa lallai da walakin kuwa domin kuwa su kansu shedu ne ba ranar da basa ganina nazo aiki.

Anan take Baban Gida ya shiga mota ya nufi gidanmu ita kuwa Hajiya Inna ta koma sashen ta amman taki a nan ta tsaya suna maida bahasi.

A bakin ƙofar gidanmu ya yi parking kuwa ya samu yaro ya aikosa kan cewa ana sallama da Hadeejatu, lokacin na dawo gida domin na ƙara kwantarwa da ƴan uwana hankali ganin yana yin da muka barsu.
Jin Hadeejatu a bakin yaron da aka aiko na tabbatar da tabbas wani daga cikin ƴan gidan aikina ne kuma ba makawa aiken Hajiya Inna ne.

Saurin fita na yi ai kuwa muka yi ido huɗu da Baban Gida, fitowa yayi bayan mun gaisa yake gayamin Hajiya Inna ce ta turosa domin a gani ko lafiya yau ban samu damar zuwa gidan ba?."

"Ayya wallahi yau mahaifiyata ce babu lafiya yanzu haka tana kwance a asibiti, ko yanzu uzurine ya mayar dani gida amman yanzu zan koma". Na faɗa iname kallonsa yayin da idanuwana suka cika da ƙwalla.

Fatan samun lafiyarta yayi min sannan ya ce "idan koma wa zanyi nazo ya wuce dani daga can."
Ba musu kuwa na koma cikin gida nace dasu A'ishah suzo muje su dibo jikin nata sannan su dawo da Baba domin ni inajin a can zan kwana.

Kayan da muke da buƙata na ɗiba sannan muka rufe gidan muka shiga mota sai asibiti.

Ko da muka shiga harta samu bacci an ɗaura mata ruwa, sai lokacin hankalina ya kwanta ganin yadda take bacci cikin nutsuwa.

Sai da a kayi sallar magarib sannan Baba dasu A'isha suka yimin sallama a kan saida safe.

★★★★★★


"Shalele kayi hanzari kazo muje hwa dare keyi ba rana ba!."
Hajiya Inna kenan dake tsaye tana kiciniyar sanya hijabi.
Fitowa ya yi daga cikin ɗakin yana ƙoƙarin ɗaura hula a saman kansa , sai wata walƙiya yake yi kamar sabon awarwari.

Kallonta ya yi sannan ya ce "muje Hajiya Inna ko baki kammala shirin bane?."
Harara ta wurga masa sannan ta ce "nafi minti 30 ina jiran ka amman yaronnan ka shige ka barni bansan me kake yi a cikin dakin ba."

"Afuwa Hajjaju, kece naga gaba ɗaya yinin yau duk kin tayar da hankalinki , haba dan Allah ki kwantar da hankalinki komai zai koma dai dai insha Allahu, kinsan wani lokacin abu yakan kasance haka."

Gaba ta yi ba tare data ce dashi komai, ƴar dariya ya yi yana me bin bayanta.

A bakin mota ya isko ta ita da Baban Gida direba suna magana ba.

Buɗe bayan motar ya yi da kansa ya shige ciki , suma ba tare da jinkirin komai ba suka shiga.


Ina zaune ni kaɗai har lokacin Mama tana bacci na sanyan ta gaba ina kallonta, sallama naji wacce ko ban tambaya ba nasan wannan muryar Hajiya Inna ce, miƙewa nayi da sauri na nufe ta haɗi da rungume ta ina meyi mata sannu da zuwa.

Amsawa take yi cike da kulawa tana tambayata game jiki da "Alhamdulillah" na amsa mata sannan taja hannuna muka nufi bakin gadon da Mama take kwance.

Idanuwana ne suka sauka saman nasa wanda gaba ɗaya banma kula dashi ba sai yanzu.

Ya yi kyau cikin yadi fari wanda ya fito da zallar madarar kyaunsa, na yi hanzarin janye idanuwana ina gaidashi , ciki ciki ya amsa man hakan be dame ni ba nasa hannu na janyowa Hajiya Inna kujera.

Lokacin ne kuma Baban Gida ya shigo hannunsa riƙe da kula da leda baƙa mai layi layi ya ajiye a gaban sannan muka gaisa dashi.

Sun jima zaune sannan suka yimin sallama suka tafiyarsu.
Naji daɗin ziyarar dasu Hajiya Inna suka kawomin ko ba komai sun nuna sun damu dani.
Har lokacin Mama bata farko ba kuwa, na buɗe kular da suka shigo da'ita domin ganin abinda ke ciki.

Soyayyen naman kaza ne jar suya a ciki sai farfesun kayan ciki daman sai cikin leda kuwa kayan marmari ne.

Farfesun da naman kazar  na ɗiba naci sosai domin kuwa rabona da abincin tun jiya da daddare wannan ne yasa na samu ci da yawa kuwa, sannan nasha ruwa na yi hamdala na yi shimfiɗa a ƙasa na yi kwance iname tunanin abokin rayuwata, eh mana abokin rayuwa domin kuwa a yanzu ba daren da bana tunaninsa kamin bacci ya yi awon gaba dani idan kuwa na samu baccin ya ɗauke ni to ba makawa sai na yi mafalkinsa.


Ƙarfe 11pm Mama ta farfaɗo na gane hakan ne ta hanyar wayar da Baba ya bani da zai tafi kan cewa zai dinga kira yaji jikin nata.

Cike da farin cikin ganin ta farko lafiya na kira Baba na sheda masa murna a gurina ba'a magana, taimaka mata na yi tayi sallolin dake kanta sannan na zuba mata ferfesun da Hajiya Inna ta kawo , da alamu taji daɗinsa ganin yadda taci da yawa sannan na bata ruwa tasha na taimaka mata ta koma kan gado.
A haka muka dinga fira jefi_jefi ni da ita har bacci ya yi awon gaba dani.

Ƙarfe 4am alarm ɗin da na saita ya tadani , ina miƙewa na haska Mama naga tana ta bacci , waje na fito na yi alwala sannan na koma na tada sallah,  sai da naji ana kiran sallar subh a masallacin dake cikin asibin na miƙe naje na tada Mama na taimaka mata ta yi sallah sannan muka zauna muna ƴar fira jefi jefi.

Ƙarfe 7am direban Hajiya Inna ya shigo ɗakin hannunsa niƙi niƙi da kaya nice na tarbosa kana na amshi kayan na ajiye gefe ina yi masa sannu da ƙoƙari.

Be daɗe ba ya yi mana sallama ya tafi , Mama nata zuba godiya haɗi da miƙa gaisuwarta a gun Hajiya Inna.

Bayan tafiyarsa bada jimawa ba Baba da A'isha suka zo su mukayi ta murna ni da A'isha kana daga bisani Baba ya yi mana sallama zaije wajen neman abinda zamu dinga sawa bakin salati, ya barmu anan da zummar duk abinda ake ciki na kira sa na gaya masa.

Nima anan nabar A'isha naje gida domin na yi wanka kuma naga tashin ƙannena sannan kuma nazo masu da ragowar naman da Hajiya Inna ta aiko mana haɗi da break fast ɗin data aiko mana.....

Za mu ci gaba a gobe.......

ƳAR MUTAN BUBARE CE!