ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 35
ANA BARIN HALAL..:
*Page 35*
**********
Da safe na tashi da wuri domin naje na gyara side ɗin ummie, sbd hafsy bata nan, a parlor na sameta tana sauraren karatun sheikh Ahmad sulaiman, cikin karatun shi na suratul YASEEN, har ƙasa na tsuguna na gaisheta, parlon na fara gyarawa sannan na wuce ɗakinta, ina cikin gyaran na jiyo muryan hajiya ummah na buga bayani wa ummie na kayan, mai gadin mu tasaka ya ɗauko mata kayan, sai bayani ta keyiwa ummie na zuwan da A.G yakeyi, abunda ya kamata da wanda bai kamata bama duk tayi dalla - dallah wa ummie, kayan takaici kaman tana mana laɓe har da cewa wai A.G tsabar so kaman zai haɗiye ni, bayan ta gama jaddada komai, tayi hanyar waje, bayan ta jawa ummie kunne akan kada ta bari ko da wasa mamie ta fahimta, shima Abba tace zata ja mishi kunne, a haka ta fita ta bar ni cike da kunyan fitowa, ina gama gyaran ɗakin na wuce kitchen, ko da na fito parlon ban kalli inda ummie ta ke zaune ba, sa kai kawai nayi na wuce ciki, ina gyarawa ina haɗa breakfast, dama yau ba girkin ummie bane, don duk mai girki tana saka na hajiya ummah, saboda haka ko bamu tashi ba ummie muna samu tayi abun breakfast, sai dai muyi lunch da dinner, ina gamawa na zuba mana a filet ɗaya da ita na fito da shi parlon, ƙasa ta sauƙo kan carpet muka fara ci, gefe ɗaya kuma na haɗa mana tea ina ta gauraya nawa don yayi sanyi, wannan ɗabi'a nane bana iya sha tea mai tsananin zafi, amma kuma da tafasheshshen ruwa zan haɗa, chan kaman daga sama na jiyo muryan ummie, "tun yaushe kuka fara magana da shi A.G ɗin? Dawowan shi yanzu ko tun kafin ya yi tafiyan"? A burkice na ɗago kai cike da tsarguwa ina zare ido, kaman ban fahimci tambayan ba nasake tambayan ummin da, "me kikace ummie"? Kallo na tayi kaɗan, sai kuma ta cigaba da abinda takeyi, bata ɗago kai ta kalle ni ba sai ta sake cewa, "ki kula da kanki da tarbiyan ki, ki ɓoye neman wa ƙawaye da ƴan'uwa har sai komai yayi ƙarfi, ni dama na daɗe da addu'an Allah ya baki miji mai nutsuwa ɗan mutumci, kuma Alhamdllh wannan yaron yana da nutsuwa, don ko nasan sai mai nutsuwa ne tafiyan su zai zo ɗaya da yayanku, Allah ya sanya alkhairi".
Tana gama faɗin haka sai naji duk abincin ya fice mun a rai, ni narasa meyasa suke farin ciki da maganan nan,.
Wunin ranan nayi shi duk a tsarge, komai sai naji yaƙi tafiya mun yadda naci buri, gashi zuciyata cike da haushin M.G take, haka dai nayita ƙunci na.
Bayan sallan magrib sai ga iran shi nan, bayan mungaisa naja nayi shiru, har zuwa wani lokaci sai yayi murmushi yace, "wato ko sannu da hanya bazaki ƙira kimun ba ko? Na ƙira ɗin ma bazaki tambaye ni yayah hanya ba kp?".
Hararan wayan nayi na murguɗa baki kaman yana gani na, a xuciyata nace , "kai daka ga zaka iya ae ka ƙira", kaman wanda yaji mai nace, sai naji sautin muryan shi yace, "nikan da na damu ae na ƙira", gwalo na mishi na sake hararan wayan, "yaya tou meye labari?" naji ya tambaye ni, murya ƙasa -ƙasa nace, "ni ban iya labari ba", murmushi yayi yace, "tou ni nabaki labarin"? Nidai shiru nayi ban bashi amsa ba, jin nayi shiru sai naji yace, "samari nawa kika taɓa yi? Mutum ɗaya dai nasani wato mijin habiba Aliyu ko"? Buɗe baki nayi cike da mamakin yayah akayi ya sani? Murmushi yayi yace, "kina mamaki ko? Tsabar son jin labarin da ya shafeki ne watarana Barr dana dame shi kina da samari? Sai yace mun shi bayaga ma kina kula kowa, don tun wani dayace yana sonki ko baku fajimci juna bane? Sai ya koma habiba, abun ya mun daɗi nace gara mishi ae da yayi gaba saboda Ayshan ta Aminu ce",
"Aminu"? Naji bakina ya furta ban ankara ba, murmushi yayi mai sauti naji yace, "sorry ban taɓa gaya miki full name ɗina ba ko? *AMINU GARBA INUWA* (AG) mummy ne ta saka mana tun muna yara nida M.G, har yanzu kuma sunan ya bimu, saboda haka sunan mijinki maigaskiya".
Tura baki nayi gaba haushin ya ƙira kanshi da sunan mijina.
"saboda haka bayan shi gaya mun su waye suka taɓa cewa suna sonki"?
Gyara zama nayi nace, "nada ko kuma har da na yanzu"? A ɗan ɗage naji muryan shi yace, "ban gane ba Eeshaa, kina nufin kina da wasu samari da kike kulawa?..... Kuma kina hira dasu?...... Akwai wanda kuma kike so?" duk naji shi a furgice yana tambaya na, dariya ce taso ƙwace mun babu shiri, ganin na samu abunda zai saka na bashi haushi sai nace, "a unguwan mu mutum biyu ne kawai, sai unguwa su zee mutum ɗaya, amma duk bana kula su, a school ne kawai nake kula wani lecturer mu da wani student da yake final year a masters, su biyun ina son su....." ae ban ƙarasa bayanin ba naji shi da sauri da kuma ɗan ƙarfi kaɗan ya buɗe muryan shi yace, "kada kimun haka Eeshaa, ina da kishi sosai, nifa ban taɓa kula wata ba, ban taɓa ganin wata nace ina sonta ba sai ke". "ni kan yanzu ma naga wani yana brgeni, addu'a ma nakeyi yace yana sona", na faɗa cike da mamakin kaina yadda bakina ya buɗe don na ƙular da shi ko zai haƙura.
"Eesha Allah bazai nufa ba, ke nawa ce ni kaɗai, zan dawo gobe insha Allahu, ya kamata Daddy su turo wurin Abba, zan samu Barrister yau muyi magana" ae ko da sauri nace, "nifa wasa nake maka, wallahi bana son kowa, kuma bana kula kowa", "Eeshaa hankali na ya tashi tsoro nakeji, idan kikaje kika fara fah? Zan dawo goben insha Allahu ayi abun da ya kamata", ae ban ɓatawa kaina lokaci ba nayi wuff nace, "please mana yayah A.G, don Allah kada ka wahalar da kanka, ba aiki kaje yi ba? Don Allah ka zauna ka ƙarasa, wallahi wasa nake yi, ka tambayi yayah ma ba'a barin mu any how muna kula samari", ajiyan zuciya ya sauƙe mai ɗan ƙarfi, muryan shi alaman aɗan shaƙe yace, "Tsoro nakeji Eeshaa, amma promise me bazaki kula kowa ba"? Murguɗa baki nayi saboda haushin wai bazan kula kowa ba, ama don kada ya dawo mun nayi sauri nace, "ehh nayi", "kinyi alƙawari ke nawa ne ko? Alhmdllh amma duk da haka zanyi magana da barrister, don komai yazama manya sun shiga ciki, don kinga nan da 2weeks zan koma, yakamata komai yazama manya sun shiga."
Nidai cike da jin haushin shi naja bakina nayi shiru, ganin da yayi babu wani haɗin kai da zan bashi ayi hiran ya saka ya mun sallama.
*********
Ƙarshen satin da muke aka kawo kayan aure da nasaka ranan raliya, murna da ɗaga wuya a wurin mamie kaman yayah, gashi babu ƙarya an zabga mata kaya kam, sai wani hura hanci itama raliyan takeyi, ita dai habiba babu um babu uhuhm, don Abba ya saka ta dole kullum da yamma tana fita tana ɗan zaga haraban gidan, cikin tan bai wuce wata biyar ba amma ta wani hau kaman ajiƙa yeast, yawancin ranaku idan tafito ita kaɗai, mukan haɗu har takan mun murmushi, nima nakan mayar mata.
A.G dai bai samu dawowa bauchi ba sai ana saura 2dys ya bar ƙasan, domin wani case ne ya riƙe shi a Abujan, gashi M.G kuma ya fita china shi da Daddy su A.G, kuma yasamu yayah Ahmad da maganan, har Alhaji inuwa yazo shi da wani abokinshi wurin Abba, sunyi magana akan a bari sai idan A.G ya gama ya dawo a saka rana, sun dai yi maganan su na manya kawai, kuma abun mamaki Abba bai sanar a cikin gida ba, illah daga shi sai Aunty Rakiya da Ummie, don ita hajiya ummah dama ita ta kawo shawaran hakan, ko Mamah da bata da matsalah Abba bai sanar mata ba, hattah hafsy bata da labari, don Abba yacewa ummie ko danginta tayi shiru sai lokaci yayi, A.G bawai mutum mai tsananin ƙiran waya bane, zai ƙira da safe, zai ƙira da dare, shiyasa abun yake bani haushi, inaga yadda maryam kafin tayi aure take shan waya, ni kuma sai wannan duskum ɗin, haka dai ya shigo bauchi shi da yayah Ahmad, idan wannna ƙarshen wata yayah Ahmad yazo, wani ƙarshen watan kuma yayah Auwal sai yazo, haka sueyi, don kada su bar chan babu kowa.
Nasan ana idar da sallan ishaa zaizo yadda yace, ina shiga sallan magrib nayi wanka na saka skirt da riga na atamfah batik, banyi wani kwalliya ba ko cika jikina da turare ba wani Humrah ne kawai na shafe jikina da shi, Fatima ce da mukaje bikinta ta bani shi mai sanyin ƙamshi, haka kuma ban wani ɗaura ɗan kwali ba sai na yafa gyale *SHANTALI* a kaina, sharr dani kuwa na fito.
A Parlor na samu ummie da Yayah Ahmad sai hafsy zaune, Ƙasan carpet na zauna daidai ƙafan yayah Ahmad, hannun shi ya ɗaura saman kaina yace, " Eeshan Gwani kin fito ne"? Turo bakina nayi gaba cike da shagwaɓa, dukkansu dariya sukayi, hafsy shugaban ƴan sa'ido tace, "yaƴah sunan shi Gwani kenan? Hala Gwanin iya soyayyah ne ko yayah"? Ta faɗa tana wani ƙyalƙyala dariya, shima dariyan yayi yace, "wannan ae Gwani ne a koto, don idan ya tsayah ba'a samun mai kada shi, kullum winning yakeyi shiyasa aka saka mishi GWANI ɗin, tou soyayyah kuma ae na lokaci ɗaya ne zai cinye wasan", ya ƙarasa dukkansu suna dariya har ummin, ummie ce tace, "yaron ae gaskiya babu laifi, yana da nutsuwa sosai, sai dai ita Ayshan ne banga ta wani zafafa ba akanshi kaman yadda naga su rasa kunya suna kulawa da nasu", ummi ta faɗa tana pointing hafsy, "gaskiya kam ummie mukan muna son namu bamu wani nuƙu - nuƙu, kaso mai sonka, kabashi kulawa kafin wata chan daban ta maka wuff da shi ta barka baki buɗe", ta faɗa tana guduwa zuwa ɗaki tana dariya, ummin ma dariyan ta sukayi ita da yayah Ahmad, sannan yayah ya kalloni ido a waje yace, "Eashan Gwani akwai matsalah ne? Idan akwai ki gaya mun tunda wuri, amma dai kam a sanina kafin ki samu nutsatstse irin A.G akwai wuyan gaske, baida problem ko kaɗan, gashi mai son gaskiya da riƙon amana, amma idan bai miki ba ki faɗa tun wuri".
"wani irin bata son shi, ae ni dai banga makusa a tare da shi ba ko kaɗan, yaro mai kyau da ilimi, gashi ya fito a zuriya masu daraja, nidai addu'a na Allah ya tabbatar da alkhairi a wannan tafiyan, "
Ummi ta faɗa, shidai yayah Ahmad ƙara jaddada mun idan bana so na faɗa da wuri, nidai bance uffan ba kawai na sunkuyar da kaina ƙasa, a haka aka ƙira sallan ishaa, fita yayi mu kuma muka shige ciki don yin sallan, anan na samu hafsy ana ta shan soyayyah a waya, ko kula takanta banyi ba na ɗauki hijab na fara sallah, don nasan tsantsan iskanci ta ga na shigo ne take wani karairaya murya tana, "Baby tou me kachi tun ɗazun? Amma dai yayah umar bai kyauta ba da bai nema maka wani abu da zaka ci ba, ae yasan ciwo yana kan kowa, sorry Baby nerh", ina jinta ta na ta wasu ƙalƙala a harcenta, nidai na maida hankalina nayo sallah na, na idar tana ta kan wayan, hararanta nayi nace, "idan kin haɗu da walakiri sai ki gaya mishi zabgegen Baby ne ya hanaki sallah akan lokaci", dariya ta kwashe da shi tana gayawa yayah ishaq abunda na faɗa, sannan ta kashe wayan ta shige toilet, na kai mintuna talatin a zaune a wurin ina wuridi, don har hafsy ta idarr tayi nata wajen ina zaune a wurin.
Muryan A.G naji da yayah Ahmad a parlor, A.G suna gaisawa da ummie nah, dafa saitin zuciyata nayi domin wani bugawa yake mun, babu daɗewa kuwa sai ga yayah Ahmad ya shigo ɗakin kallona yakeyi fuskan shi cike da seriousness, "kifito AG yana Parlor idan kuma kinga baki ra'ayi tou ko gaya mun yanzu zan sallame shi ko zai samu attack ne, ni nafi son farin cikin Eesha na akan nashi", sunkuyar da kaina nayi ina murmushi, shima murmushin yayi ya juya ya fice.
Tashi nayi ina dariyan maganan yayah Ahmad, wai kada yasamu attack, tou akan me? Haka dai na fita zuwa parlon, samu nayi hafsy ta ajiye mishi zoɓo da cin-cin a gaban shi, ina fitowa kuma ta wuce tana ƙunshe baki ta shige ɗakin ummie, wanda nake jin muryan yayah Ahmad a ciki, na daɗe da zama tukun na gaishe shi murya chan ƙasa, ajiyan zuciya yayi sannan naji yace, "mummy tana gaishe da ƴarta Eashaa, Eeshaa beauty", ya faɗa ƙasa-ƙasa kaman baya so wani yaji, don ni ma kaɗan kaɗan naji shi, ɗago kai nayi na kalle shi, don naji kunya da ban tambaye shi yayah take ba? amma da sauri na maida kaina ƙasa saboda ina ɗago kai yana ɗaga mun giran shi sannan ya kashe mun ido ɗaya, tura baki nayi gaba ina gunaguni, domin bai san kunyan da yake sakani ba idan ya wani ɗaga giran nan ko ya kashe mun ido, gashi dama wasu irin ido yake da shi masu sani jin ɗumi a jikina, "I luv u kike faɗa mun ƙasa -ƙasa"? naji shi yana faɗa, nan ma da sauri na ɗago kaina na dube shi baki a buɗe, "nifa cewa nayi sai kai ta ɗagawa mutum gira bakajin kunya", dariya yayi yace " kuke fah, ba gashi kim buɗe baki kin gaya mun idona suna gigita ki ba", kallon shi nayi nace, "nifa bawai nace suna firgitai bane, kawai dai naga da kunya mutum ya dinga kashe ido yana ɗaga gira, ni kunya yake sakani",
Idon shi ƙurr akaina yace, "tou nima ki mun naji yayah kikeji, ina so nima naji kinyani ko kaɗan ne", ya faɗa still yana sake ɗaga mun giran na shi, kukan shagwaɓa na fara mishi ƙasa -ƙasa ina ƙunƙuni na, dariya yayi kaɗan ya taso ya dawo kujeran kusa dani, "Eeshaa nah don Allah kada ki susutani a parlon ummin mu, wallahi idan baki bar kukan nan ba zan tayaki,"
Ɗago kaina nayi da sauri jin yayi ƙasa da murya kaman zaiyi kukan, kallon shi nayi ido waje nace, "nifa ba kuka nakeyi ba, please ka kuma chan kada yayah ya fito".
Ajiyan zuciya kawai yayi ya ƙura mun idon shi duka da suke lumshe, "Eeshaa kina da kyau sosai, banda ni banga wanda yafi ki kyau ba a duniyan nan, idon ki masu kyau kawai nawa ne yafi naki kyau", hararan shi nayi ina kallon shi nace, "kafini kyau?" ɗaga kai yayi alaman haka yake nufi, hararan shi nayi nace, "nafika dogon hanci fah," murmushi yayi yaa kan kallo na da lumsheshhen idon shi, bai ce komai ba sai idon daya kura mun yana wani smilling, hararan shi nayi na sauƙe idona ƙasa, don gaskiya ne yana da wani mahaukacin kyawawan ido, tun ba yau da ya matso kusa dani kuma yayi maganan kyaun ido yasaka na kalle shi da kyau, ga idon manya da su amma baya iya buɗesu dukan su, "nidai ka koma chan", na faɗa ina kawar da kaina gefe.
Hancin shi ya ɗan shafa kaɗan yana kallona, "Beuty kinsan kyaun hanci na kuwa? Baki san yafi dogon hanci kyau ba, kalla kiga hancin mu fa kusan iri ɗaya ne fah dake, don kema naki daidai ne mai kyau, don har ya kusa iso nawa a kyau", dariya ne ya ɗan suɓuce mun, "ni ban taɓa jin mai yaba kyaun shi ba sai kai, kuma har kana tunanin ina mace ka fini kyau" na faɗa ina maida kallon na fuskanshi, marairaice mun fuska yayi cike da alaman shagwaɓa yace, "Allah akwai wata ƴar Eathoupia da muke course ɗaya da ita, kullum sai ta ɗauki photo na idan ina zaune, har friend ɗinta ƴar India ce ita kuma, wata rana ta daure tazo har inda nake ta zauna, chan sai tace, "an taɓa gaya maka irin baiwar kyaun ido da kake da shi"? Kallon ta nayi shiru bance komai ba, sai ta cigaba, "friend ɗita AFRAH kana mata kyau, tana so kuzama friends da ita, amma ta kasa gaya maka", tou ni tunda ga ranan na ƙara yadda ni mai kyau ne, saboda ƴan eathoupia da india har suka ga kyau na, ae kuwa kyaun nan ya kai inda ya kamata ya kai", ya ƙarisa faɗa yana wani shafa fuskan shi, ido shi kuma akaina.
Lokaci ɗaya naji wani mumunan ɓacin rai, wanda har akan fuskana ma bai ɓuya ba, kallon shi nayi ya ƙura mun ido nace, "kuma kayi accepting ɗinta kun zama friends ɗin"?
Girgiza kai yayi alaman a'a, sanan ya buɗe baki har lokacin cike da wani basarwa yana wani ya mutsa fuska yace, "ina zan accepting mata? Kalan duk ranan duniya ta dinga kallona tana yaba kyau na? Ko amsawa friend ɗin nata banyi ba, tashi nayi na wuce room ɗina, a zuciyata nace, "wallahi baku isa ba, sai nazo naji daga bakin Beauty nah, idan haka ne tou sai naji gaskiyan batu, idan bakiga kyauna ba kuma sai na koma nayi accepting ɗinta, don ima son naji ance ina da kyau, da kyaun ido", ya faɗa yana kara shigar da idon shi cikin nawa.
Ajiyan zuciya mai ɗan Ƙarfi na sauƙe, wanda har sai da yasaka shima ya sauƙe, "ita ɗin tana da kyau ne"? Na tambaye shi, ɗaga kai sama yayi alaman ehh, ɓata rai nayi nace, "kenan dai ta maka kyau"? Girgiza kai yayi alaaman a'a , harara na aika mishi da shi, "mekake nufi tou? Nasan ae ta burge kane shiyasa baka manta fuskanta ba", na faɗa ina tura baki gaba, du raina ya ɓaci.
Buɗe baki yayi ya saka hannu a haɓan shi yace, "nifa ke kaɗai nake ganin kyaunki, kawai ina so ke danafi so da ganin kyaunki naji daga bakinki kafin wasu kuchakai su dinga gaya mun, nafi son jin nako, ina da shi ko bani da shi"? Ya faɗa muna ara haɗa ido da shi.
Yamutsa fuska nayi sannan nace, "kana da shi kaɗan, amma dai baka wani fini ba", na faɗa ina kallon yatsun hannun shi da yake ɗan lanlanƙwasa su.
"Nifa nayi tunanin nafiki kyau wallahi, tou idan na koma zanje na samesu sumun bayanin yadda zan fahimci nawa kyaun, don ni tunani na nayi irin sosai ɗin nan ne".
Da sauri nace, " ba sai ka sake neman bafa, kana da kyau sosai, idonka ma mai kyaune sosai, kada ka sake kula su, kaga ance kai mutumin kirki ne kada kuma azo a ga kana kula mata", na faɗa kaman zan masa kuka.
Dariya yayi sosai yana lumshe ido, sannan ya ɗan sunuya sosai da kanshi yace, "dare yayi zan gudu wurin mummy, gobe insha Allahu zanzo muyi sallama, sai naji sauran bayanim, don ma ɓoye miki ne, tave ma tana sona, amma nafi so naji daga gareki, idan sonki yafi burgeni, tou xanyi warning ɗinta, idan kuma ke baki sona sai na duba yayah natan yake", ya faɗa yana miƙewa tsaye, dama sanye yake da wasu jean da shirt mai layi layi, ya mish kyau sai ƙamshi yakeyi, nima tashi nayi tsayen don jin da nayi yace bari dai ma na koma sai na ƙirata mu gaisa a waya don kada tace na shareta, kin san sun bani number wayan su".
Ɓata rai nayi nayi gaba don rakashi zuwa bakin ƙofan fita, hanya na bashi ya fita, yana fita ya tsaya ya maida hannayen shi cikin aljihun wandon shi ya karkatar da kanshi gefe kaɗan ya ƙura mun ido, duk narasa mai yake mun daɗi, a hankali na kalle shi fuskana cike da damuwa nace, "ka ƙirani idan ka isa zan gaya maka wani abu", risinar da kanshi yayi kaɗan yace "angama Beauty nah, inaga muna gama waya da ita zan ƙiraki, ko kuma sai munyi da ke"?
Bansan lokacin dana fara buga ƙafana a ƙasa ba, "nikan bana so ka ƙirata, ka Ƙirani sai nagaya maka tukun", na faɗa ina shirin mishi kuka.
Matsowa yayi kusa dani yace "mummy kawai na miki alƙawarin zan kula a duk matan duniya sao na ƙiraki, ko sister na yau ta kalle ni sai na ranƙwasheta ballantana ta mun magana, ina shiga ɗaki ke zan ƙira ranki ya daɗe".
Dariya ya bani babu shiri na juya cikin parlon da sauri, shima ina jin sautin dariyan shi.
Kaiiii jama'a nidai babu wani dariyan da zan tsaya yi, duk kun gajjiyar dani da typing yau, nayi fah sosai, saura naji wata tace na tau ma ɗan tsurut ne.
Jinajina wa
Jewel
Mrs xerks
Mum fodio
Hassan 80k
*AUNTY NICE*
managarciya