ANA BARIN HALAL: Fita Ta Farko
ANA BARIN HALAL:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE
*BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM*
Don Allah ina bada haƙurin ganin chanjin sunan danayi, daga *AMINAN JUNA* ya koma *ANA BARIN HALAL*......
Da fatan zaku mun uzuri, na chanja ne sbd wani babban dalili, nagode
*PAGE* 1
A hankali Hajiya Ayshaa ta miƙe daga tsakiyan gadon ta jiki duk a sanyaye tayi hanyar window ɗakinta dake kallon haraban gidan ta saka hannun ta wanda yasha jan lalle mai bala'in kyau ta ɗan yaye labulen ɗakinta, idon ta cike da hawaye take leƙen haraban gidanta, inda yake cike maƙil da ƴan kai amaryah, duk da tsiyar da ƙawayenta da suke zaune a ɗakin suke mata na rashin dauriyar da tayi na tafiyan ƴar na ta ƙwaya ɗaya dal kaman rai gidan mijinta, ita dai bata bi ta kansu ba hankalinta yana ga kallon jama'an da ke ta shiga motoci don zuwa kai amaryar gidan mijinta, a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya ta juyo tana kallon ƙawarta data dafa Kafaɗanta, cikin ƙasa-ƙasa da murya ta furta, "*Aunty Nice* ban san yayah zanyi na jure tafiyan Maamah ba", lokaci ɗaya kuma idon ta yana ƙara cikowa da hawaye.
Cike da tausayawa na irin soyayyan dana gani a fuskan ta na dafa kafaɗanta nace, "ƙawata ae aure ba mutuwa bace, ba kuma rabuwa bace, ae abun kiyi farin ciki ne ki ƙara godewa ubangiji daya nuna mana auren Maamah, wanda ko wacce uwa take fata da burin taga ta aurar da ƴarta lafiya, mudai fatan mu Allah ya basu zaman lafiya, Allah kuma ya fitowa na baya da mazaje nagari, yadda Maamah ta samu," batare dana bar inda take ba na sake riƙo hannunta nace mata, "haƙuri zakiyi ƙawata, haka aure yake, kuma idan an kwana biyu zakiji sauƙin abun, banda abunki ƙawata ae dama dole mu rabu da ƴaƴan mu watarana," jijjiga kai tayi alaman hakane ta riƙo hannu na tace, "Aunty Nice na shaƙu da Maamah sosai, sai kuma ina ganin kaman bayan zu bane lokacin daya kamata tayi aure".
Hararanta nayi cikin wasa, na juya ina duban ƴar'uwarta da suka fito ciki ɗaya, wanda ta shigo tana kallon Aysha tana tambayanta kowa ya fita a ƙawayenta masu zuwa kai amaryar? Ayshaa ta juya ta kalli ƙawayen ta da suke zaune a kan gado wasu a kan kujeru wasu a ƙasa, ta sake juyawa ga ƴar'uwarta tace, " masu zuwan duk sun fita, sune a cikin motan Hajiya Hadiza, dama mutum Uku ne zasuje",
Cikin hanzarin sister nata ta juya da fita daga ɗakin tana cewa, "Dama Goggo ce ta ce na tambayeki"
Haka dai muka cigaba da wunin mu har zuwa magrib, inda dayawa aka fara haraman watsewa, inda kowa ka ganni a cikin ƙawayenta hajiyoyin kansu ne, daga wanda driver ke jiranta sai wanda ita da kanta ta tuƙo kanta, biki ne dai irin bikin ƴan boko masu ji da naira, wanda komai kushewan ka kaje wurin wannan wunin sai ya burgeka, ga shi komai cikin burgewa da ilimi akayi shi, wanda duk wadata ta ɗaukaka irin na Hajiya Aysha batayi wani events masu yawa a bukin nan ba, liyafa kawai tayi haɗaɗɗe jiya jumma'a a Event Center na Bauchi, mai matuƙar ƙayatarwa, sai yau da aka haɗa ɗaurin aure da wunin bikin ɗiyarta, *NANA KHADIJAH (MAAMAH)*
Har zuwa gate ɗin gidan Hajiya Ayshaa ta rako mu, tana ƙara godiya wa bakinta da suka zo, a haka kowa zakaga ta buɗe motanta ta shiga, ko kuma drivern ta ya tuƙata, fuska ɗauke da murmushi ta juyo tana ƙara riƙe hannu na tana cewa, "Aunty Nice gaskiya nagode da ƙoƙarin da kika mun, nagode da zumunci Aunty Nice, Allah ya nuna mana auren Nabeelah da rai da lafiya", nima fuska cike da murmushi na dubeta cikin farin ciki nace, "Ameen ya rabbi Ƙawata, fatan mu Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a mai albarka, Allah yasa baɗi mudawo taron suna",
Cikin rausaya da yanga wanda na lura halittan Hajiya Ayshaa ne, ta amsa mun da "Ameen ya rabbi ƙawata", sannan nace "tou yanzu ƙawata zan baki sati biyu ki huta, gajjiya ya bar jikinki, sai ki bani labarin da kika mun alƙawari, duk da dai nace nadai na rubutu yanzu" na faɗa fuska na cike da murmushi ina dubanta, Hjy Ayshaa cike da rausayar daya bi jikinta, ta lumshe kyawawan idonta a hankali kuma ta buɗe tana duba na, itama fuskanta cike da murmushi tace, "Aunty nice tawa, ae ko bai kai 2weeks bama zaki ganni, da zaran jama'a sun mun sauƙi xaki ganni har gida insha Allahu, idan kin koma gida ki gaida mun da Ɗana *BAPPAH NUHU, da ƴata NABEELAH* ki kuma miƙa mun saƙo a jama'an mu na *MUYI NISHAƊI DA NOVEL 2, har ma jama'an mu na TABITAL PULAKO* kice musu saura idan sunji labarin suyita zagina", tafaɗa tana ƙara murmushin fuskanta zuwa dariya, nima dariyar nayi nace, "insha Allahu zan ja kunnen su, duk da ma kina group ɗin kina kallon komai da jin komai", mukayi sallama na fito daga gate ɗin gidan, ita kuma ta juya zuwa wurin wasu ƙawayenta cike da rausaya, ni kuma hannu na cike da kayan tsaraban bikin da ta haɗani dasu, dayake ba mota bane gare ni balle driver, sai danayi ɗan tafiya mai ɗan nisa zuwa bakin titi, sbd unguwar tasu ta *G.R.A* wurin babu cikar abun hawa, ina isowa bakin titi na tsaya ina ɗan gyara zaman glashin fuskan na, na duba ƙafana ina kallon takalmina mai kyau na sallan bana da saura kaɗan wata taja mun asara ta sace mun shi, daga ganin jama'anta da suka zo daga cikin gari ne, wanda sukayi maƙil ata can boys quaters, wata taso ta samfe mun shi ta fallashe ni, don ni banyi niyan sayan takalmi a bana ba, atoh yana yin rayuwar nan ae sai kanayi kana tattali, na kalli dogon riga na danaje Hanco ta zizaramun wani haɗaɗɗen ɗinki, zanina dana saya a wurin *JUWAIRI* itama a *MUYI NISHAƊI* take, matar badai iya zaɓawa mutum kalan zani mai kyau ba, ajiyar zuciya nayi na ƙara duban kaina nace, "oh mace har mace amma babu mota", dariya nabawa kaina naƙara gaba kaɗan na tari adaidaita, mun ɗanyi jayayyah da shi akan ina neman ya kaini a ɗari uku, amma firr yaƙi wai sai ɗari bakwai, kaman zanyi kuka haka na shiga, sbd wasu wurin an fara sallan magrib, ina iso gida na zazzage jakan da aka haɗani da shi, cike da farin ciki nace, "shiyasa nake son bikin masu kuɗi ƴan boko, komai nasu a tsare, wato komai dai da kika sani an zuba a ciki, su turmin zani ne sallaya ne, hijab ne, kai komai dai dakika sani an zuba aciki, kuma dama tun ana saura 1week biki ta aiko mun da bocket ɗin su cincin da sauran tarkacen kayan buki, kai matar nan Hajiya Ayshaa babu laifi, dama haka wasu Allah yake haɗaka da su, sai kudawo kaman ƴan'uwa, yanzu sanin da nayi wa Hajiya Ayshaa tun lokacin da nake rubuta *BADARIYYAH* amma ji nake kaman mun shekara 40 tare, Allah kabar mana zumunci Ameen.
Ringing ɗin waya nane ya farkar dani a bacci, wurin ƙarfe 9:46am na safe, narasa dalilin dayasa ban saka shi a silent ba, haka raina bai soba na jawo wayan zan kashe, sai naga *ƘAWATA* ɓalo-ɓalo yana yawo akan screen ɗin wayata, tashi nayi zaune na ɗauki wayan, cike da yangan ta naji muryan ta tana mun sallama, "Aunty nice barka da safiya", nima cikin fara'ar da ta wadata fuskata lokaci ɗaya na maida mata da gaisuwan ta, bayan mun gaisa take cemun yau insha Allahu wajen 11am zata zo idan ina gida, babu ɓata lokaci na dirƙo a gado na nayi toilet, a gaggauce na shiryah mukayi breakfast, a take kuma na ɗaura abincin rana bamai wuya ba saboda na samu daman zama da baƙuwa ta Hajiya Ayshaa, domin hiran da zamuyi da ita yau na musamman ne, duk da wataran takan ɗan tsakura mun kaɗan daga labarinta, muyi shawara a kan wasu abun, nima nagaya mata wasu daga cikin labarina, amma yau na musamman ne, tunda tace mun tun daga ranan haihuwar ta zata bani labarin kanta, har zuwa yau ɗin nan, Rice and stew nayi, sbd ta taɓa cemun favourite ɗinta kenan.
Ayshaa matar arziki matar kirki mai alƙawari mai gaskiya, wuraren 11:00am ɗin kuwa ta tuƙo kanta zuwa gidana, cikin farin ciki na tarbeta har parlor na ta zauna, cike da fara'ar da kullum yake kan fuskanta ta dubeni tace, "Aunty Nice kinsan haka kawai kike burgeni? har wataran nakanji dama ciki ɗaya muka fito, ina son ƙamshi, ina son gayu, gashi Aunty Nice kullum cikin ƙamshi da gayu kike, ni ba gidanki ba kuma ba jikin ki ba, kin san kullum kikaje gida na sai Maamah tace kinzo," ina dariya nace "haba ƙawata ina ƙamshin yake, duk kawu na Tinubu ya takura mu ɗan turaren ma nakasa sayan dayawa yanzu, manage kawai ake ƙawata",
Kallo take bin ko ina a falo na takeyi da idon ta, " Aunty Nice kedai ki gode Allah da yayi ki ƴar gayu da son ƙamshi, kinsan ƙamshi rahma ne," "hakane na faɗa ina tashi don zuwa kitchen kawo mata abun sha,"
"Aunty nice don Allah ga wannan tou ki shiga da shi babu yawa" naji tana faɗa,
Bucket ne ɗan madaidaici, wanda yake ɗauke da dambun nama a ciki, ɗauka nayi na buɗe ina nuna mamaki fal a fuskata ina cewa "ƙawata wannan uban naman fa daga ina? Ke baki gajjiyawa ne kam"? "Wallahi wanda nasaka akayi ne wa Maamah na manta ban ɗiba miki ba, kinsan ban nutsuba wallahi sai cikin kwanakin nan nagani, tou dama nayi niyyan keda su Hajiya Hadiza da Zainab zan ɗiba muku, babu yawa ae", inji hajiya Ayshaa, godiya na mata na ɗauka nakai kitchen na adana, bayan na kawo mata abun sha, na nemi wuri a ɗayan kujeran da yake kallonta na zauna, "Ranki ya daɗe ina labari? Na furta ina kallonta fuskana cike da murmushi.
Juya idonta tayi cike da yanga da ruba, a hankali ta maida kallon ta ƙasa, kaman wanda take nazarin wani abu akan carpet ɗin, har zuwa wani lokaci kuma sai tayi dogon ajiyan zuciya, ta ɗago ta kalle ni.
*AUNTY NICE*
na daɗe banyi rubuta ban san ko na manta tsarin rubutun ba, ko zan iya kawo labarin Ƙawata Aysha yadda zai ƙayatar da ku, yakuma ilimantar da ko, ko kuma alƙalamin zai ce mun No, gamu nan dai tafe da labarin Ayshaa
*AUNTY NICE
managarciya