WATA UNGUWA: Fita Ta 28

WATA UNGUWA: Fita Ta 28

BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS

 

Alhaji Saminu ya yi ƙwafa sannan ya juya riƙe da 'yar a hannunsa, ya fice daga gidan a kufule, ya hau motarsa ya ta da ta da ƙarfin tsiya.

 

Yana tuƙi yana saƙe-saƙe a ransa 'yanzu kenan ina zan kai wannan jemammiyar yarinyar? Wane mataki zan ɗauka akan Hanifah.?'

 

Ya sauke ajiyar zuciya ya yi ƙwafa "Kina wasa da ni Hanee Baby, ko da yake baki san waye ni ba, haka zalika baki san kirarina ba, ni ne fitilar sharri da ko ba mai nakan kai safe."

 

A haka ya ci gaba da karatun wasikar jaki har ya isa ƙofar gidan da ya zaɓawa yarinyar don ya zama muhallinta kuma kejin da zai rufe asirinsa daga fallasa.

 

Bayan doguwar gaisuwa tsakaninsa da masu kula da gidan marayun, ya nemi ganawa da shugaban gidan, ya yi masa bayanin muradinsa ya sanar da shi cewa ya tsinci yarinyar ne a gefen hanya yayin dawowarsa daga ofis. A haka ya ɗora shi akan keken ɓera, aka buɗe wa yarinyar file ya cike ya ƙara gaba, cike da tunanin ɗaukar fansa.

 

Bayan kwana biyu ya gama shirya shirinsa tsaf. Tafiya ya yi unguwar Dagarma ya haɗa kai da yan daba don aiwatar da shirinsa akan Hanee.

 

 

Wataranar Asabar da yamma Hanee da ƙawarta Farida ne suke tafiya a cikin wani layi, Hanee tana sanye da hijabi iya gwuiwa, ta yi shigar kamala, da alama dai ta shiryu. Da ma yan magana sun ce duniya tafi Bagaruwa iya jima.

 

Farida sai cin-cingum take yi ƙas-ƙas, ta gyara zaman ƙaton glass ɗin da ya kusan mamaye  rabin fuskarta, ta kalli Hanee.

 

Ta ce "Gaskiya Mutuniyar kin ba ni kunya, kuma kin saka na ji kunya, da kika zo nemana da wannan shigar."

 

Hanifa ta ɗago idanunta, ta zuba mata su.

"Ban fahimci inda kalamanki suka dosa ba."

 

"Sarai kin fahimta, kawai rainin hankali ne irin na sabbin ustazai zaki yi mini. Wai ke yanzu me kike nufi kin zubar da makaman yaƙinki kin daina bariki kenan?"

 

Hanee ta yi murmurshin yaƙe "Kusan haka, domin yanzu na ɗauki darasi daga abin da ya faru da ni a rayuwa. Sai dai abu ɗaya ne zai iya dawo da ni duniyar bariki shi ne ɗaukar fansa. Bana so akai ga hakan shi ya sa na zo neman taimakonki. Ina zamu je mu yi magana a sirrance?"

 

Farida ta yalwata fuskarta ta murmurshi ta ce "Idan sirri kike buƙata mu tsaya a nan kawai."

 

"Baki da hankali ne Reedah? Wane sirri ne zai samu akan hanya, inda kowa zai iya tsintar zancen da muke yi?"

 

 

Ta jefe ta da murmushi a karo na biyu.

"Gaskiyarki ne, kowa zai iya tsintar zancen, sai dai ba zai yi nasarar tsintar ma'anarsa ba daga shuɗawa."

 

Hanee ta yi yar dariya "Shi kenan mu tsaya a nan, nama ga ba hayaniya sosai."

 

Bata jira cewar Reedah ba ta ɗora zancenta "Ina neman hanyar da zan koya wa Alhaji Saminu hankali ne, shi ne dalilin da ya sa ban goge lambarsa ba. Kin ga ke bai sanki ba, ki taimake ni ki cika mini burina na ƙarshe kafin mutuwata ta riske ni."

 

"Sarai kin sani, Ni bana harka da ire-iren waɗannan alhazzan, amma saboda amincin dake tsakaninmu zan yi miki. Me kike so ayi masa."

 

Hanee ta yi ƙayataccen murmurshi tare da faɗar "Nagode ƙawata, zan baki lambar wayarsa da muhimman bayanai a kansa. Ina so ki ƙuntata rayuwarsa, ya zamana cewa naman dake cikin ruwan mai akan wuta ya fishi walwala. Ina so ki saka shi a masifa sa'annan ki fallasa asirinsa a idanun da suke ganin darajarsa sosai. Da son samu ne ma, ki yi duk yadda zaki yi ki shafa masa wannan cutar ta zamani."

 

Dariya sosai Reedah ta yi ta ce "Ta kwana gidan sauƙi, indan wannan ne ki kwantar da hankalinki tamkar kina cikin jirgin sama mai ya ƙare. Na yi miki alƙawarin cewa daga kanki Allah Saminu ya ƙare yaudara."

 

Suka tafa cike da nishaɗi, suka ci gaba da tafiya. Sun zo dai-dai titi suka yi sallama Reedah ta juya ta fara tafiya.

 

 Gif! Wani sauti mai ƙarfi ya ratsa kunnenta ta juyo a kiɗime.

 

"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un! Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un!!"

 

"Ku bi shi, ku dakatar da shi."

 

Wadannan sautukan ne ke kawowa kunnuwanta ziyara, idanunta suka fara disashewa. Idan har ba ƙarya idanunta suka faɗa mata ba, kamar Hanifah take gani kwance a cikin jini tana kokawa da numfashinta.

 

Ai da gudu ta ƙarasa wurin, a lokacin har an fara kewaye Hanifar da take famar ɗaukar rai. Mai motar da ya buge ta kuwa ya gudu, kamar da gayya ya aikata wannan aikin.

 

Ta tallabo kan Hanifar tana faɗar "Hanee Baby ki tashi, kada ki mutu pls. Wani ya taimaka a kaita asibiti don Allah."

 

Hanifah sai kallonta take tana yunƙurin yin magana, dakyar ta amayar da kalmomin da ta naɗo a harshenta ta ce "Ki cika alƙawarinki."

 

 

Ummu Inteesar ce