203:Ɗan majalisar waƙillai za mu zaɓi wanda ya cancanta ne-----Alhaji Ado Abubakar
Kujerar Majalisar Wakilai; Dole Mu Zabi Matashi Mai Kishin Kasa A Chanchaga
An nemi al'ummar karamar hukumar Chanchaga da su tabbatar a zabe mai zuwa sun zabi Alhaji Ado Abubakar domin shi ne matashin da ya nuna kishin cigaban karamar hukumar Chanchaga. Wani malamin addinin musulunci a minna, Malam Murtala Abdullahi ne yayi kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Malamin ya cigaba da cewar ya kamata yan siyasa su canja tunani, domin bai yiwuwa jama'a su zabe ka sannan ka rika daukar hakkin su kana kafa wani sashin da ba su baka kuri'a ba. Dan majalisar da ke wakiltar Chanchaga a yanzu tun zuwan sa majalisa ba wani gurbin aiki da za a ce ya samarwa koda mutum daya daga yankin nan, duk lokacin da wata dama ta zo masa sai ya karkatar zuwa wani sashin na daban, lokaci yayi da al'umma zasu takawa irin wadannan yan siyasar burki.
" Mun gamsu kuma mun amince da fitowar Alhaji Ado Abubakar neman wannan kujerar, domin mun san matashi ne mai kishin karamar hukumar Chanchaga, da bai san ko ina ba face karamar hukumar mu, muna da tabbacin idan ya samu dama sai samar da cigaban da za mu yi alfahari da zabin shi a wannan kujerar".
Malam Murtala ya jawo hankalin matasa da su guji shiga bangar siyasa, akidun bangar siyasa ne ke sanya yan siyasa ba su ganin darajar su a tafiyar siyasa. Kowa ya tabbatar ya mallaki katin zabe domin muna da tabbacin zabe mai zuwa yin anfani da aringizon kuri'a ko satar akwati ba zai yi tasiri ba.
Alhaji Ado Abubakar matashin dan siyasa ne da ya taba neman kujerar majalisar wakilai a jam'iyyar APC, sai dai ba samu nasarar zaben ba, wanda a wannan karon ya nuna sha'awar sake neman takarar kujerar a zaben 2023 mai zuwa a jam'iyyar APC mai mulki a jihar Neja.
managarciya