Har Yanzu Ina Takara a Jam’iyar PRP Saboda Akida Nake Siyasa Ba Don Kasuwanci Ba----Nisiru Milo
Dan takarar dan majalisar tarayyar Nijeriya dake son ya wakilci Sakkwato ta Kudu data Arewa cikin jam’iyar PRP a zaben 2023, Honarabul Nasiru Jibril da aka fi sani da Milo ya musanta managanar ya sauya sheka zuwa APC domin shi siyasarsa ta akida ce ba kasuwanci ba.
Nasiru Milo a zantwarsa da wakilinmu a Sakkwato ya ce wannan magana ce kawai aka yi wadan da suka sauya sheka dai sun sauya “amma ba gaskiya ba ne a ce duk wanda yake takara a PRP ya bari, mu manan PRP daman wadan da suka yi haka suna da niyar yin haka kuma sun yi, wannan hakkinsu ne su yi abin da suka ga dama, bai kamata su yi mana kudin goroba; mu ba za mu canja ba muna son jama’a su sani mun shiga PRP ba don mu yi kasuwanci ba, sai don akida da kawo cigaba ga jama’a,” a cewarsa.
Ya cigaba da cewa kowa dana sa ra’ayi da tunani wadanda suka yi a ganinsu hakan ne yafi, kuma siyasar Nijeriya haka ta gada mutane da zaran sun ga ba za su samu biyan bukatarsu ba sai su sauya sheka, ‘mukan ba haka muke ba, bama siyasa don kasuwanci sai domin kawo cigaba a kasarmu da al’ummarmu,’ kalaman Honarabul Nasiru Milo.
A nan gaba za ka iya sayar da gaskiyar da mutane suka sanka da ita? Ya ce “wallahi da in yi haka gara nabar siyasa gaba daya, in dai sauya sheka don a bani wani abu ko don bana cin zabe gara nabar siyasar gaba daya, na aminta zan yi wannan takarar ne domin al’ummarmu a Sakkwato ta Kudu da Arewa na bukatar canjin wakilci ganin wanda ke saman kujerar bai yi wani abin a zo a gani ba don cika muradun jama’a nake wannan takarar ba don kai na ba, don haka nasha alwashin ba zan ba su kunya ba,” in ji shi.
A farko jam’iyar APC ta fitar da takarda ta hannun mai baiwa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko shawara kan harkokin yada labarai Bashar Abubakar cewa PRP ta rushe duka ‘yan takara a jam’iyar PRP a Sakkwato sun bari sun koma jam’iyar APC karkashin jagorancin dan takarar gwamna Honarabul Sa’idu Muhammad Gumburawa.
Hakan ya sa Nasiru Milo ya nisanta kansa da sauya shekar da dan takarar gwamnan ya yi don shi baya cikin wadan da suka yi wannan tafiyar zai tsaya a tare da al’ummarsa.
managarciya